Makarantun boko sunyi rangwame a kan kudin makaranta

Makarantun boko sunyi rangwame a kan kudin makaranta

- Sakamakon halin koma baya da tattalin arziki ke ciki, wasu mammalakan makarantun boko sun yanke shawarar yin rangwame na kaso 50% ga dukkan iyayen da suka biya kudin shekara daya a lokaci daya

- Wasu iyayen suna ci gaba da matsa lamba a kan ma’aikatan makarantun don suyi wa yayansu tsalaken aji saboda guje ma bayan kudin makaranta na shekara daya

- Wasu makarantun kudi sun gama yanke shawara a kan shirinsu na rage kudin magaranta saboda iyayen da suke tunanin cire yaransu su komar dasu makarantun gwamnati.

Makarantun boko sunyi rangwame a kan kudin makaranta

Kamar yadda koma bayan tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da shiga halin matsi, wasu mammalakan makarantun boko sun shirya yin rangwame na kaso 50% ga dukkan iyayen da suka biya dukkan kudin shekara daya a lokaci guda.

KU KARANTA KUMA: Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara

Wannan yazo ne a lokacin da wasu iyayen ke ci gaba da matsa lamba a kan ma’aikatan makaratu da su yi wa yaransu tsalaken aji domin guje ma biyan kudin makaranta na shekara daya.

Bisa ga binciken jaridar Vanguard, kamar yadda iyaye ke cire yayansu daga makarantun kudi, wasu mammalakan makaratun kudi sun yi rangwame wanda zai ja ra’ayin iyaye domin su rage zafin halin wahala da ake ciki.

A daya daga cikin makarantun dake Ipaja, rangwamen shine, idan ko wani iyaye ya iya biyan kudin makaranta na shekara daya kafin shekarar ta kai, zasu sami rangwamen kaso 50% a shekarar da zai biyo baya.

KU KARANTA KUMA: Wani Alhaji yayi wa marainiya ciki a jihar Sakkwato

Shugaban wata makaranta a Agege, Lagas, wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa wasu iyaye wanda koma bayan tattalin arziki ya taba, sunje gurin mammalakan makarantun kudi suna neman ayi wa yayansu tsallaken aji ba tare da sun kula da matsayin karatunsu ba.

Wasu iyayen suna ganin cewa tsallaken aji zai zama sauki a kan sun a biyan kudin makaranta na shekara daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel