Villareal za ta ziyarci Real Madrid a gasar La Liga wasan mako

Villareal za ta ziyarci Real Madrid a gasar La Liga wasan mako

Villareal za ta ziyarci Real Madrid a gasar La Liga wasan mako na biyar da za su kara a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba.

Madrid tana mataki na daya a kan teburin gasar da makin 12, yayin da Villareal ke matsayi na shida da maki takwas.

A ranar Lahadi Real Madrid ta yi kan-kan-kan da Barcelona a yawan lashe wasannin La Liga 16 a jere, bayan da ta ci Espanyol 2-0.

Sauran wasannin mako na biyar a gasar ta La Liga da za a yi a ranar Laraba, Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a Camp Nou.

Barcelona tana mataki na biyu da maki tara, ita kuwa Atletico maki takwas ne da ita tana matsayi na hudu a kan teburin La Liga.

.Celta de Vigo da Sporting Gijon

Real Sociedad da Las Palmas

Granada da Athletic de Bilbao

Source: Legit

Online view pixel