Wata mata ta mutu ranar jana'izar mamanta

Wata mata ta mutu ranar jana'izar mamanta

Matar wacce akace tanada kimanin shekaru 30 a duniya an bayyana cewar ta sanya mutuwar maman nata a zuciya ne sosai saboda shakuwar datayi da ita.

Wata mata ta mutu ranar jana'izar mamanta

Pauline Wangari tare da mahaifiyarta Esther a kwance.

Maccen da abun ya faru da ita, wacce ake cema Pauline Wangari, an rufeta a kusa da kabarin mamanta. Maman nata mai suna Esther Wangari wacce take da shekaru 72 72 a duniya, ta mutune 15 ga watan satumba, wanda ba'a san dalilin mutuwar nata ba.

Wani wanda ke gaba-gaba a hidimar birnewar mai suna Jackson Muriuki, ya bayyana cewar, " Yarinyar ta shaku da maman nata sosai. Ita yarinyar takan kwashe lokaci mai tsawo tana kwance a kan gadon maman nata tun bayan da mahaifiyar nata ta rasu 3 ga watan Satumbar shekarar 2016".

Sauran mutanen dake zaune a unguwar Nyeri sunji mamakin faruwar al'amarin, inda suke cewar kila yarinyar ta mutune sanadiyar kidimewar da tayi.

Haka kuma, wata 'yar uwar ta mai suna Rose Mwangi tace; " Tasha maganinta kuma ta tambayin abincinta a kichin kafin ta koma gida. Sai kuma daga baya muka ganta bata cikin hayyacinta, mukai ta kiranta bata amsaba ashe ta riga ta mutu.

Haka kuma, 'yan kyauyen sun bayyana mamakinsu akan mutuwar na Paulines.

Asali: Legit.ng

Online view pixel