Zani ba Wada, Faleke ayyukan yi - Gwamna Bello

Zani ba Wada, Faleke ayyukan yi - Gwamna Bello

- Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello yayi alkawarin samarma abokan hamayyarsa tsohon gwamnan jihar Idris Wada da kuma James Faleke ayyukan yi

- Bello yace tunda ya hau karagar mulki jihar ta samu rarar kudi naira biliyan N1.4 daga albashin ma'aikata

Zani ba Wada, Faleke ayyukan yi - Gwamna Bello

wada

Gwamnan jihar Kogi, wanda aka tabbatarma cin zabensa yayi alkawarin shiryawa da duk mambobin All Progressives Congress (APC) masu korafi dake jihar da kuma dan takarar PDP na jihar, Idris Wada. Bello yayi magana lokacin da yake bikin nasarar da ya samu, yace ya fara kokarin hada kansa da Wada da James Faleke, mataimakin dan takarar gwamna Audu Abubakar wanda ya rasu yayin zaben Nuwamba 2015. Ya kara da cewa:

KU KARANTA:Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi

"Zan mika goron gayyata garesu, bisa gaskiya ma na riga na fara tuntubar wasunsu. Zani basu ayyukan yi cikin jihar", inda ya kara da cewa basu ayyukan zai kawo saurin ci gaban jihar

" mun iske tsarin gwamnati wanda ke da ma'aikata barkatai wadanda kudaden albashinsu kadai ya kai yawan biliyan N3.00. Abinda ke hannunmu bai wuce naira biliyan 2.0 ba. Ba yarda zamu ci gaba da haka inda bashin albashin ma'aikatan gwamnati ya kai na watanni biyar yayin dana kananan hukumomi ya kai watanni 12

Zani ba Wada, Faleke ayyukan yi - Gwamna Bello

" Mun sami rage albashin da yawan naira biliyan 1.4. Shawara ce mai nauyin dauka amma zamu ci gaba da yin haka".

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel