Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi

Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi

A karo na farko a Najeriya, kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa da sauran jama’a tanadi; wannan akan zaben Gwamnan jihar Kogi mai suna Yahaya Bello.

Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
Alhaji Yahaya Bello da kotun koli tace shi ne halattaccen gwamnan jihar Kogi

Yadda aka saba a baya shi ne, idan ana sauraron shari’ar data danganci manyan mutane, ko kuma za’a yanke hukuncin irin wannan shari’ar, toh ba’a yarda jama’a su shiga koda farfajiyar kotunan, wasu lokutan ma har da yan jaridu ake hanawa.

KU KARANTA: Kotun koli ta tabbatar da Yahaya Bello a matsayin gwamna

Misalin irin wadannan shari’un sune; shari’ar da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki yake fuskanta kan bayyana kadarorin karya tare da mataimakinsa Ike Ekweremadu a kotun ladabtar da ma’aikata da babbar kotun birnin tarayya. Sai kuma shari’ar da aka shigar da tsohon minister Abba Moro gaban kotun birnin tarayya kan aikata miyagun laifi.

Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
Lauyoyi yayin da suke fita daga kotu

Sai dai abin mamaki, a wannan karon, sai ga shi kotun koli ta tanadar ma masu sha’awar sauraron karar da fararen kujerun roba a farfajiyar ta, kusa da dakin sauraron kara. Sa’annan kotun ta samar da talabijin guda biyu don kallon shari’ar kai tsaye ga mutanen dake wajen kotun a tashar gidajen talabijin na kasa.

Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
Jama'a yayin da suke kallon shari'ar a talabijin

Yadda aka saba a baya shi ne, idan mutum ya shiga asalin dakin sauraron kara, sai jami’an tsaro su tambaye ka katin sheda, kuma su tambayeka dalilin ka na zuwa kotun, idan basu gamsu ba sai ku kore ka.

Shari’ar Kogi: Kotu tayi ma magoya bayan yan siyasa tanadi
cincirindon jama'a a farfajiyar kotun koli

Sai dai a wani labarin kuma, majalisar alkalai ta kasa ta fara binciken alkalan kotuna masu matsayi daya dake bayar da hukunce hunkunce masu sabani da juna. Jaridar Vanguard ta ruwaito alkalin alkalai na kasa mai shari’a Mahmud Mohammed ya bayyana haka a ranar Litinin, 19 ga watan satumba a yayin kaddamar da bikin shekara shekara na alkalan kotun koli. Mai shari’a Mahmud ya tabbatar da duk alkalin da aka kama da laifi, toh zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel