Sabon girgizan kasa ya afku a jihar Kaduna

Sabon girgizan kasa ya afku a jihar Kaduna

Sabon girgizan kasa da ya afku a kauyen Kwoi a karamar hukumar Jaba dake jihar Kaduna ya tursasa mazauna kauyen barin gidajensu, jaridar Puch ta ruwaito.

An rahoto cewa al’amarin ya faru ne dare da girgiza mai karfi. Wani girgizan kasa ya faru a ranar 19 ga watan Satumba da misalign karfe 3 na dare.

Da yawa mazauna kauyen sun fara barin kauyen.

Bayan al’amuran sun afku, makarantu a garin sun rufe, yayinda aka umarci dalibai da suka dawo daga dogon hutu da su koma gida.

A cewar daya daga cikin yan kauyen da suka bayyana abunda ya faru: “Girgizan kasan yau yayi kara sosai, ya fi wadanda suka afku a baya kara. Wannan ya tursasa wasu makarantu rufewa. Sun mayar da dalibansu gida.

KU KARANTA KUMA: wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya

A yanzu haka Dr Idowu Abbas, shugaban sashen masu karantar ilimin kasa na jami’ar jihar Kaduna, ya bayyana cewa ci gaban girgizan kasar na iya sanadin afkuwar babban girgizan kasa.

Ya shawarci gwamnati da ta sanya ido soasi a kan kauyen don gudanar da sahihin bincike. Jihar Kaduna ta fuskanci girgizan kasa guda biyu a kwanakin baya.

KU KARANTA KUMA: Yahaya Bello yayi alkawari ga marigayi Audu Abubakar

A ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba, ta shekara 2016, da misalign karfe 1 na rana, girgizan kasa ta afku a kauyen Kwoi dake karamar hukumar Jaba na jihar Kaduna.

A ranar Litinin, 12 ga watan Satumba, girgizan kasan ta kuma afkuwa, wanda ya bar mazauna kauyen cikin rudani da tsoro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel