Yahaya Bello yayi alkawari ga marigayi Audu Abubakar

Yahaya Bello yayi alkawari ga marigayi Audu Abubakar

- Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello yayi alkawarin ci gaba da tsarin marigayi gwamnan jihar Audu Abubakar

- Bello ya kuma rogi abokanan takarar sa a zaben gwamnan jihar Kogi

- Idris Wada da kuma James Faleke- da su shiga cikin sikin don ganin jihar Kogi ta inganta

Yahaya Bello yayi alkawari ga marigayi Audu Abubakar
Yahaya Bello da Audu Abubakar

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya yi alkawarin ci gaba da hangen nesan marigayi gwamnan jihar Audu Abubakar kan mutanen jihar Kogi.

Da yake Magana a gidan gwamnan jihar Kogi da ke Abuja, bayan nasarar sa, Bello a yayinda yake addu’a ga ruhin marigayi gwamnan yace ma zai ba ruhinsa kunya ba.

“Ina so na mika godiyata ga mutanen jihar Kogi da suka bani daman da zan bauta masu a wannan aiki, ba daban kokarinsu da sadakarwar shugabanmu, marigayi Prince Audu Abubakar, Allah yaji kansa ba da ban kasance a nan ba,” cewar Bello.

KU KARANTA KUMA: Mulkin Arewa a kasar Najeria tun 1960

Da yake Magana ga marigayi Audu, sabon gwamnan jihar Kogi da aka daura yace: “Ina so na tabbatar mai da cewan: ruhin ka na a raye kuma bazan baka kunya ba. Hangen nesan da kake wa jiharmu, zan kica maka har ma fiye da tunaninka; jihar Kogi ba zata taba zama irin da ba.

 “Ina so nayi amfani da wannan damar nayi kira ga dukkan yan uwana, tun daga kan dan’uwanmu, tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Idris Ichalla Wada, jihar Kogi mallakinmu ne gaba daya, kazo mu hada hannu ka kuma bani shawarar uba nagari.

 “Ina kira ga dan uwana, mai girma James Abiodun Faleke, da ya zo mu hada hannu mu gyara jihar Kogi."

KU KARANTA KUMA: Matukin jirgin shugaba buhari, kyaftin Chinyelu

Babban kotun Najeriya ta kaddamar da Bello a matsayin gwamnan jihar Kogi, a ranar Talata , 20 ga watan Satumba.

Nasarar na say a zo bayan dogon gwagwarmaya da ya sha tare da sauran yan takara-Tsohon gwamnan jihar Idris Wada da kuma James Faleke, abokanan takaran marigayi Audu Abubakar, a neman kujerar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel