Aisha Buhari da Michelle Obama sun hadu

Aisha Buhari da Michelle Obama sun hadu

- Aisha Buhari ta hadu da Michelle Obama a haduwarsu na farko don gudanar da wani abu a USA.

- Haduwar tasu tayi kyau sosai, inda ko wacce daga cikin su tayi kyau.

Aisha Buhari da Michelle Obama sun hadu

Aisha Buhari dai itace mace ta farko a Najeriya kuma itace matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato shugaba mai ci a yanzu a kasar Najeriya. Haka kuma Michelle Lavaughn Robinson Obama, itace mace ta farko a kasar Amurka, kuma matar shugaba Barrack Obama, shugaban kasar Amerika mai ci a yanzu.

Aisha da Michelle sunyi haduwarsu ta farko a Broadway a wani taron da Michelle obama ta shugabanta, domin taimakama karayun 'ya'ya mata yaci gaba a duniya.      Matan shuwagabannin guda biyu sunyi shiga kusan iri daya, wanda hakan ya sanya ake tunanin ko tela daya yayi musu dinkin da suka sanya. Inda Aisha Buhari ta sanya kallabi mai kalan gwal da kuma kayan da tasa mai kalar gwal da kuma fulawa ajiki mai kalar baki.

Aisha Buhari da Michelle Obama sun hadu

Haka kuma, Michelle Obama ta sanya doguwar riga itama mai kalar baki tare da ratsin fulawa a jikin kayan mai kalar gwal, sannan kuma aka sanya raga akayi hannu da wuya a jikin rigar.

Dukkan matan shugabannin sunyi kyau, amman mutum dayace kawai zata iyacin gasar. Har ilayau kuma, wacecce ta cinye wanka a taron da akayi a Broadway, Aisha Buhari ko Michelle Obama? Bari muga kuri'arku a nan kasa.

Aisha Buhari da Michelle Obama sun hadu

Taron dai da akayi a Broadway wanda aka gudanar a Bernand B. Jacobs Theatre, sannan anyi shine tare da matan shuwagabannin sauran kasashe da zimman nuna kalar jibi, " da matan dake kula da mutane a wajen cin abinci, " Mugawe" dakuma " kyawawa": da kuma wakar sarautar Carole".

Michelle tace, idan mutane suka samu labarin mata wa'anda basu zuwa makaranta, sunaso su taimaka. Sannan kuma akan matan shuwagabannin kasashe, duk yawancin mu da muke cikin wannan dakin taron ya kamata muyi kokarin hada kan al'umman mu domin muga mun dauki mataki akan wa'dannan yara matan.

Saboda mutane zasuji kiraye kirayen da zamu dunga yi musu, idan har muka nuna musu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel