Direban Tirela ya murkushe wani a Legas

Direban Tirela ya murkushe wani a Legas

Wani direban babban mota, Tirela kirar IVECO, Kabiru Ademola ya tattake wani mai tafiyan kafa har lahira a unguwar Mushin na jihar Legas.

Direban Tirela ya murkushe wani a Legas

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne daidai lokacin da motar ta kwace ma direban da misalin karfe 2.30 na dare ranar lahadi, 18 ga watan satumba, sanadiyyar haka ne motar ta tattake wani mai tafiya a kafa mai suna Kamoru Ibrahim. Jaridar Punch ta ruwaito cewa babbar motar ta bugi wata karamar mota kirar Toyota Camry dake ajiye a gefen hanya.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) tare da yansanda ne suka kawo dauki a wajen hatsarin. Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar legas Rasak Fadipe yace jami’ai daga ofishinsu na Isolo ne suka fara isa wajen hatsarin, ya kara da cewa da suka fahimci abin yafi karfinsu ne suka gayyaci LASEMA.

KU KARANTA:Babbar hatsarin motar Tirela ta auku

Wani jami’in LASEMA da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na dare.

“Hatsarin ya faru ne a kan titin Agege, Mushin. Motar na dauke ne da duwatsu, amma sai direban ya shiga tsere da wata babbar mota, ana cikin haka ne, sai motar da kufece masa, daga nan sai ya afka ma wani mutum dan shekara 38 Kamoru Ibrahim, mutumin ya makale a kasar motar, said a mukayi amfani da kayan aiki muka iya ciro gawarsa daga kasar motar. Sa’nnan motar ta bugi wata karamar mota kirar Toyota Camry dake aje gefen hanya.” Inji Shi.

Jami’i mai magana da yawun yansandan jihar Legas yace sun kama direban motar, ya kara da cewa sun mika gawar mamacin zuwa asibiti don gudanar da bincike akan sa. “Motar ta kauce daga kan hanya ne, sai kuma ta take mutumin, nan take ya mutu,” inji ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel