Zargin cin mutuncin yan gudun hijira ba gaskiya bane - Minista

Zargin cin mutuncin yan gudun hijira ba gaskiya bane - Minista

Ministan kyautata rayuwar mata da kula da jin dadin jama’a na tarayyar Najeriya Hajiya A’ishatu Jummai Alhassan, ta ce babu gaskiya a korafe-korafen cin zarafi da gallazawa mata da yara mata a sansanonin ‘yan gudun hijira na jihohin Arewa maso Gabashin kasar.

Wannan na zuwa ne biyo bayan ziyarar rabon kayan abinci da atamfofi da katifofi da kuma kayan masarufi ga mata masu shayarwa da ta kai jihohin Yobe da Borno, domin bincikar wadannan zarge-zarge.

A ganawar da wakilin majiyar mu ya yi da wasu daga cikin mata da suka ci gajiyar tallafin, Malama Zainab Dungus ta tabbatar da wannan matsayi na binciken ministan na cewa babu gaskiyar a batun cin zarafi ko gallazawa mata da yara mata da aka ce ana yi a sansaninsu. Yayin da su kuma Maryam Ali da Fanta Mohammed da bata jima da samu da na miji a sansanin ba ta yaba da tagomashi da suka samu daga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hannun ministan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel