Wani Matashi ya damfari Bishop Oyedepo,Dantata da sauransu

Wani Matashi ya damfari Bishop Oyedepo,Dantata da sauransu

Yan sanda sun kama wani wanda ya kammala makaranta, ya karanci Political science Jehu Kwasu wanda ya damfari wasu manya a Najeriya inda yayi basaja da sunan Bishop Mathew Kukah.

Jaridar punch ta ruwaito mana cewa Kwasu ya bayyana masu cewa ya samun kimanin miliyan 5.7 daga wasu manya-manyan a Najeriya da ya damfara ta hanyar yin basaja da sunan wani. Jehu Kwasu ya bayyana cewa ya damfari Oyedepo da wasu manya a kasar nan.

Wani Matashi ya damfari Bishop Oyedepo,Dantata da sauransu
Jehu Kwasu

Wadanda ya damfara sun hada da Bishof Oyedepo shugaban cocin living faith, sai shugaban kamfanin honey well Oba Otudeku, Admiral Nduibisi Kanu da shahararren dan kasuwa Alhj. Aminu Dan tata.

Yace" na anshi N500,000 daga Otudeko, Nduibisi ma N500,000, haka Bishof Oyedepo 50,000 da miliyan 2 da na ansa hannun Dan tata, kuma na ansa hannun Gen. Wushishi da sauransu.

Na bude asusun ajiya a bankin GT, inda na bude da sunan Bishof Kukah, nayi rejista layin wayata da suna nan amma nayi amfani da hoton Kukah, dan Koda na kira, wadanda nakira zasu ga hotonshi ya fito.

Kwasu wanda ya kasance da ga margayi James Kwasu na cocin Anglican ya ta ba amfani da sunan baban sa ya tsaso kudi gurin Gomnan Katsina Masari a lokacin yana shugaban majalisa. Dan shekara 25 ana zargin sa da ya anshi kudaden saboda yan gudun hijira.

" Na samu an man Fasfot da sunan Bishof Kukah wanda nayi amfani da shi gurin bude asusun ajiya a bankin GT, kudaden da na samu ina amfani da katin ATM gurin cire wa.

Wani Matashi ya damfari Bishop Oyedepo,Dantata da sauransu
Bishop David Oyedepo

Kwamishinan babban birnin tarayya Muhammad Musty yace yara na sun kama Kwasu bayan korafin da Bishop Kukah yayi kan lamarin.

Mun samu takardar korafi da Bishof Kukah ya rubuto kan zargin Yaron da yin basaj da sunan shi gurin tsatso kudi gurin manyan mutane, sai na tura yarana su kamashi, ya saba da irin wadan nan laifukan dan haka ina shawartar jama'a da sudena amsa sakonnin Email ko Kiran wayar da basu sani ba.

Kwasu wanda aka yanke ma hukuncin zama gidan wakafi na wa 2 a gidan fursuna na Abuja, ya bayyana haka ranar juma'a 16 ga wata satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel