Fasto yayi kokarin tafiya kan ruwa,sai dai ya bi ruwa

Fasto yayi kokarin tafiya kan ruwa,sai dai ya bi ruwa

- Fasto yayi kokarin tafiya kan ruwa sai ya nutse

- Yayi domin nuna shi wani makusanci ubangiji ne

- Amma, sai dai ya tashi a lahira

Fasto yayi kokarin tafiya kan ruwa,sai dai ya bi ruwa

Wani fasto dan shekara 35 mai sun ,Frank Kabele ,ya rasa rayuwarsa yayinda yak e kokarin yin abinda annabi Isa yayi. Rahotanni sun ruwaito cewa Kabele ya fada ma jama’ansa cewa zai iya yin irin mu’ijizar da annabi Isa yayi a cikin injila. Domin yin hakan, sai ya je kogin kasar Gabon da ke babban birnin Kasar Libreville.

KU KARANTA: Kiristoci su daina saki, inji Fasto Crist Oyakhilome

Ikirarin yin amfani da ayar Matthew 14:22-33 da ke cikin injila, Kabele yace an yi masa wahayin cewa idan yanada imani sosai,zai iya yin abinda annabi Isa yayi. Idanuwan shaida sun bayyana cewa Kabele ya kai jama’arsa kogin . y ace musu zai tsallaka kogin Kombo estuary da kafa. Kogin da yake daukan mintuna 20 a tsallake da kwale-kwale. Amma fara tafiyan ke da wuya ,Kabele ya nutse,sai dai ya tashi a lahira.

Wannan bas hi bane na farko da zai faru a nahiyar mu ta afrika ba. A gidan dabbobin dajin da ke Ibadan, wani mai ikirarin cewa shin annabi ne yace zai yi abinda annabi dauda yayi ta shiga cikin garken zakuna. Duk da cewan masu kula da dajin sun yi masa gargadi,amma yak I sauraronsu ya share su. Mutumin zagaye da jama’a suna son ganin ikon Allah, ya shiga cikin kejin zakunan. Amma ko minti daya bai yi ba, zakunan sukayi biji-biji da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel