Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo

Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo

- Wani mai amfani da shafin Facebook ya watsa hotunan gurbarattun hanyoyin da ke yankin kudu maso yamma, jihohin Igbo

- Wannan ya tayar da kura akan shin laifin waye wannan

Yayinda yan kabilan igbo suke kukan neman yancin kan biafra saboda tunanunsu na cewa gwamnatin tarayya ba tayi da su, da alamar cewa akwai aiki da yawa a gabansu idan aka zo maganan hanyoyinsu.

Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo

Wani mai suna Blossom Emechebe ya watsa wasu hotunan hanyoyi a yankin kudu maso yamma kuma yayi rubutu kan yadda hanyoyi suka gurbace a garuruwan igbo.

Ta ce : “Babu hanya ko daya a yankin kudu maso yammacin najeriya. Wannan hanyan Enugu- Onitsha ne. Shin Gwamnoni da yan majalisan dokokin tarayya ba za su taimaki jama'an su ba?

KU KARANTA:An kashe mutane 23 yayinda sojoji da yan bindiga suka shiga barin wuta

“Canji ya fara da kai idan kai watsa wannan hoton har sai shugabannin mu sun tashi tsaye.

Wannan magana da tayi ya tsunguli yan najeriya da dama inda wasu suke tuhumar gwamnatin tarayya da share yankin, sauran kuma na sukan yan siyasan kabilan Igbo wadanda suka sa hakan ya cigaba.

Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo
Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo
Gurbatattun hanyoyi a jihohin Igbo

Asali: Legit.ng

Online view pixel