Farashin kayayyakin abinci ya sauka kasa

Farashin kayayyakin abinci ya sauka kasa

- An samu faduwar farashin wasu kayayyakin abinci a kasuwar Agege Darosha dake Lagos

- 'Yan kwanaki bayan shagulgulan Sallah, 'yan kasuwa na kukan rashin kasuwa

- Jama'a na danganta wannan da tashin farashin wasu kayayyaki da kuma matsin tattalin arziki da ake fama dashi

Farashin kayayyakin abinci ya sauka kasa
Kayayyakin abinci

An sami tashin farashin kayayyakin abinci tun farkon wannan shekarar ya zuwa yanzu dalilin abubuwa kamar su karin kudin mai, tashin farashin dala da kuma rashin biyan albashin wasu ma'aikata wadanda suka jaza rashin kudin saye-saye. Amma ga alama abin zai canza.

Legit.ng ta ziyarci Kasuwar Agege Darosha dake jihar Lagas a ranar Assabar 17 ga Satumba inda ta gano cewa yayin da aka sami tashin farashin kayayyakin abinci kafin Sallah da kuma lokacin Sallah, yanzu farashin kayayyakin sun sauko.

KU KARANTA: Albishirinku yan Najeriya: hauhawar tattalin arziki ya fara saukowa

Wani mai saida barkono yace, farashin ya tashi lokacin da kowa ke bukatarsa, amma ya sauko bayan Sallah domin raguwar bukatar shi.

Tumatari da barkono sunyi tsada kafin Sallah, amma yanzu mutane na iya saye. Ana saida kwandon tumatur N10,000 kafin Sallah, amma yanzu ya sauko zuwa N6,000-10,000. Farashin ya danganta ga girman kwandon, kyawon tumatarin da kuma mai saidawa. An saida kwandon barkono kan farashin 15,000-N17,000, amma yanzu ya sauko zuwa N10,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel