Alhazan Najeriya 18 sun rasu a hajjin bana

Alhazan Najeriya 18 sun rasu a hajjin bana

Jimillar alhazan Najeriya 18 ne suka rasu a hajjin bana daya gudana a kasar Saudiyya, inji jaridar Premiu Times.

Alhazan Najeriya 18 sun rasu a hajjin bana

Alhazan sun fito ne daga garuruwan Kwara, Kogi, Bauchi, Taraba, Niger, Kaduna da babban birnin tarayya Abuja, sa’annan cikin su akwai wasu yan Najeriya amma mazauna kasashen waje.

Shugaban kwamitin lafiya na hukumar kula da Hajji, Ibrahim Kana yace, alhazai guda biyu sun mutu a Madina, ciki har da yar shekara 40. Uku sun rasu ne a Muna, inda 13 suka rasu a Makkah, ciki har da wata mai tabin hankali.

KU KARANTA:Aikin Hajjin bana: Saudiyya ta hana shiga da Goro

Sai dai Kana ya danganta karancin mamatan ga samun sahihin kulawa da alhazai sukayi daga kwamitin lafiya. Kwamitin kula da lafiyar yace ya duba lafiyar mutane sama da 21,000 tun farkon fara Hajjin bana, inda ya gano mata masu ciki su biyar.

Zuwa yanzu dai an kammala kasha 95 na hajjin, don wasu alhazan ma sun fara dawowa gida Najeriya tun a ranar 17 ga watan Satumba.

A satin data gabata, Kana ya fada yan jaridu cewa alhazan Najeriya su dubu ashirin ne suka samu kulawa a asibitocin su dake Madina da Makkah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel