Rikicin Neja-Delta: Najeriya za ta hada-kai da Kasar Amurka

Rikicin Neja-Delta: Najeriya za ta hada-kai da Kasar Amurka

– Tsageranci a yankin Neja-Delta na kawowa Najeriya ciwon kai

– Kasar Amurka za ta taimakawa Najeriya wajen wanzar da zaman lafiya a yankin na Neja-Delta

– An yaba da kokarin Najeriya wajen kawar da Boko Haram

Rikicin Neja-Delta: Najeriya za ta hada-kai da Kasar Amurka
Wani daga cikin yan kungiyar Niger Delta

Ana shirin ganin kawo karshen rikicin yankin Neja-Delta na Najeriya, Mai ba Kasar Amurka shawara game da harkokin tsaro Susan Rice ta gana da takwarar ta na Najeriya Manjo-Janar Babagana Monguno (Mai ritaya) a fadar White House ta Amurka domin ganin yadda Kasar Amurka za ta ba Najeriya goyon baya na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yankin Kasar.

Shugaba Muhammad Buhari ya hallara Kasar Amurka tare da mukarraban sa zuwa taron Majalisar dinkin duniya da za ayi. Kasashen biyu sun yi amfani da wannan damar wajen tattauna batutuwan Kasashen. Amurka da Najeriya sun tattauna game da yadda za a kara samun hadin kai tsakanin juna. Vanguard ta rahoto cewa an tattauna yadda za a ga an samu kwanciyar hankali a yankin da Tsageru ke ta fasa butatan man Kasar.

KU KARANTA: Shure-shure kurum Boko Haram take yi Inji Sojin Najeriya

Kwanan ne dai Sojojin Kasar suka kashe wasu Tsagerun guda 23 har lahira, ta kuma karbe makami fiye da 50 daga hannun su. Rundunar ‘Operation Crocodile smile’ da ke yankin Neja-Delta ne dai ke wannan aiki. Manjo-Janar Ibrahim Attahiru wanda shine kwamandan Runduna ta 82 da ke Enugu yace, Soji sun raunata wasu Tsagerun da dama. An rusa sansani har 38 na tsagerun, an kuma ci nasara rusa matatun da ba su bisa ka’idar Kasa.

Amurka ta kuma yaba da namijin kokarin da Sojojin Kasar suka yi wajen kawar da Boko Haram. Mai ba Amurka shawarar tsaro Rice ke kuma cewa dole a nemawa wadanda fitinar ta auka da su kayan more rayuwa na zamani, daga muhalli zuwa su ruwan sha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel