Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin daure Zakzaky

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin daure Zakzaky

– Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa tace ba za ta so tayi katsalandan ba gama da bincike lamarin rikicin Shi’ar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ke yi ba

– Gwamnati tace ana kula da El-Zakzaky a gidan da yake daure

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin daure Zakzaky
Shugaban Kungiyar Shia, Ibraheem El-Zakzaky

A Ranar Juma’ar nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin ya sa ta ke rike da Shugaban Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) na ta Shi’a Ibrahim El-Zakzaky har yanzu. Ministan harkokin waje na Kasar Geoffrey Onyeama yayi wannan jawabi a sakatariyar Majalisar dinkin duniya da ke Birnin New York. Ministan waje na Kasar yace Gwamnatin Muhammadu Buhari ba za tayi shisshigi ba.

Ministan harkokin waje na Najeriya Geoffrey Onyeama yace Gwamnatin Tarayya ba za tayi katsalandan ba cikin binciken da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ke yi game da lamarin. Premium Times ta rahoto Minista Onyeama yana cewa Gwamnati za ta kyale doka tayi aiki kamar yadda ya dace.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram

Gwamnatin Jihar Kaduna dai ta fitar da binciken da kwamitin da aka nada su duba rikicin suka gabatar. A rikicin Shi’ar da Soji da ya faru a bara, an halla ‘yan shi’a fiye da 300 a Garin. Ministan Harkokin Kasar wajen Najeriya yace sai Gwamnati ta duba binciken kafin ta dauki wani mataki. Onyema ya bayyana cewa Ministan Shari’a na Kasar zai yi nazari a kan binciken, kana a dauki matakin da ya dace.

Minista Onyema ya bayyana cewa tabbas, ana kula da lafiyar Sheikh Zakzaky. Lauyan sa, Femi Falana dai yace Sojoji sun yi ma daya daga cikin idanun sa dameji. Sojoji dai sun hallaka ‘yan Shi’a fiye da 300 a watan Disamban bara lokacin da su ka hana Shugaban Hafsun Sojin Kasar Tukur Buratai wucewa. Daga nan kuma aka kama Zakzaky da matar sa aka daure a gidan maza! Tuni Kotu ta hana belin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel