Alhazan Najeriya 18 suka rasu tal-in-tal a hajjin bana

Alhazan Najeriya 18 suka rasu tal-in-tal a hajjin bana

–Mahajjatan Najeriya 18 ne suke rasa rayukansu a hajjin banan da aka kammala

–Hukumar hajjin tarayya wato National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) ce bayyana haka

–Marigayaun yan jihohin Kwara, Kogi, Bauchi, Taraba, Niger, Kaduna,da Abuja ne.

Alhazan Najeriya 18 suka rasu tal-in-tal a hajjin bana

Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa jimillan mahajjatan da suka rasu a hajjin bana 18 ne

Marigayaun yan jihohin Kwara, Kogi, Bauchi, Taraba, Niger, Kaduna,da Abuja ne, duk da cewan akwai mazauna kasashen waje a cikin su.

Game da cewar shugaban gamayyat likitocin hajji, Ibrahim Kana, mutane biyu sun rasu a Birnin Madina, 3 a Muns ,kuma 13 a Makkah. A ciki akwai wacce bata da isasshen lafiyan kwakwalwa.

KU KARANTA: Alhazan 10 daga Najeriya sun rasu a Saudiyya

Kana ya kara da cewa wannan shine mafi karancin rasuwan mahajjata a cikin shekaru byar din da suka gabata. Ya jingina hakan ne saboda kula da tsafta da kuma ilimantar da mutane akan lafiya da kuma likitoci kwararru.

Ibrahim Kana ya bayyana cewa Gamayyar likikocin hajjin sun yi jinyan akalla mutane 21,000 daga farawan hajjin kuma sun sami masu juna biyu 5 duk da gargadin da aka yi. Sun yi jinyan su ne a asibitoci da ke Makkah da Madina a kasar Saudiyya.

Kana, kasha 95 cikin darin mahajjatan da suka gabatar da ibadah wannan shekara sun fara koma wa gida.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel