Zakarun kungiyar Liverpool sun lallasa Chelsea a gida

Zakarun kungiyar Liverpool sun lallasa Chelsea a gida

Kwallayen da aka jefa ma Chelsea daga kafar Lovren da Henderson kafin zuwa hutun Rabin lokaci sun taimaki Liverpool inda suka lallasa Chelsea a gida da ci 2-1 ranar Juma'a 16 ga watan Satumba.

Gabzawar da akayi ta hasashe tun kafin doka wasar ta ka sance kamar yadda aka tsammace ta, wadda aka nuna kwarewa, karfi guda, iyawa da jajircewa a yayin wasar.

Liverpool sun fara taka ledar da kyau, inda suka samu suka jefa kwallon farko a mintuna 17 da fara wasar inda Levron ya ci kwallon.

Zakarun kungiyar Liverpool sun lallasa Chelsea a gida
Chelsea vs Liverpool

Liverpool sun sake jefa kwallo ta 2, wadda Henderson ya zura kayatacciyar kwallo a mintuna 36 wanda mai tsaron ragar na Chelsea Courtuis  ya kasa cire wa, wanda yaja magoya bayan na Chelsea suka kama bakin su.

Duk kungiyoyin sun tafi hutun rabin lokaci inda Liverpool suke cin Chelsea ci 2-0

Bayan matsin da Chelsea tayi bayan hutun rabin lokaci , Chelsea sun samu damar zura kwallo 1 wadda Matic ya taimaka Costa yaci, amma lokaci yayi karanci yayin da wasar ta kare 2-1.

Asali: Legit.ng

Online view pixel