Jose Mourinho yayi magana akan rashi kwazon Pogba

Jose Mourinho yayi magana akan rashi kwazon Pogba

- Paul Pogba ya kasa nuna kansa a wasanni 2 da Manchester ta doka amma Mourinho yace ba damuwa.

- Kocin yace da kasar faransa ya doka wasanni da yawa ba da dadewa ba.

- Pogba ya dawo kungiyar Manchester a matsayin dan wasan da yafi kowa tsada a duniya.

Mai horarwar Manchester United Jose Mourinho ya kare Paul Pogba kan rashin kwazon da yake nuna wa bayan dawowarshi filin na Old Trafford.

Paul Pogba baya taka leda da kyau tun dawowar shi kungiyar ta Manchester United. Na musamman yace kudin da aka biya dan sayen Pogba da United tayi ba wani abu da ne.

Jose Mourinho yayi magana akan rashi kwazon Pogba
Paul Pogba

Pogba ya doka wasa da kyau a wasar shi ta farko, amma tun bayan wasar shi da Souhthamtom be kara yin wani abun azo a gani ba, magoya bayan kungiyar sun koka da haka.

Amma Mourinho yace magoya bayan kungiyar suyi hakuri, su tuna Pogba be samu wani hutu ba tun bayan gama wasar Euro 2016.

Jose Mourinho yayi magana akan rashi kwazon Pogba
Mourinho

"Pogba ya samu doka wasar karshe a gasar Euro, kuma ba wani hutun kirki ya samu ba tun bayan gasar, yayi kokari a wasar shi ta farko, amma sauran be doka su kamar na farko ba." amma na yadda da shi, saboda nasan wane irin dan wasa ne, kuma nasan shi mutum ne mai burin cin nasara, dan haka wasar shi zata dawo haka ma kungiyar zasu dawo da wasar su mai kyau.

" Ze Iya wasa inda nake sa shi a gasar Premier league kuma ze Iya bugawa in da ya buga a wasar Feyernoord banda matsala kan wurin da ze taka leda.

In zaku Iya tunawa Pogba beyi wani abun azo a gani ba a wasar da Mancity ta doke United a gida da kuma wasar da Feyernoord ta doke United din, amma Mourinho ya kara jaddadawa Pogba a tsakiya ze Rika doka wasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel