Gwamnati zata yi ma Kanu kisar gilla-inji IPOB

Gwamnati zata yi ma Kanu kisar gilla-inji IPOB

Kungiyar yan asalin mutanen Biafra (IPOB) ta fasa kwai, inda take zargin gwamnati da shirin kashe shugabanta Nnamdi Kanu a cikin gidan yarin da yake daure ranar 1 ga watan Oktoba.

Gwamnati zata yi ma Kanu kisar gilla-inji IPOB
Nnamdi Kanu

Kungiyar ta fitar da bayanin haka ne ta hannun masu magana da yawunta Emma Nmezu da dakta Clifford Iroanya, a ranar alhamis 15 ga watan satumba, inda a ciki suka soki lamirin gwamnati na yin watsi da shigar da Kanu kotu da ta fara shirin yi, tare da nufin kashe shi a ranar cikar Najeriya shekaru 56 da samun yanci.

Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar na zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari das akin wani ta’adda Kabiru Umar (Kabiru Sokoto), kuma kungiyar ta caccaki shugaban kasa kan rashin yi ma kotu biyayya bayan tayi umarnin a saki Nnamdi Kanu. Tace “shin gwamnatin bata gamsu da kwarewar kotunan ta bane? Shin gwamnati ba zata jure bin doka da oda bane? Da har zata fara shirin kashe Kanu kisar gilla? “menene hikimar da tasa gwamnati ta gwammace ta saki dan ta’adda da yayi ma jama’a kisan kiyashi fiye da yin biyayya ga umarnin kotu”

KU KARANTA: Zanga Zangar Biafra: Kotun Ta Fitarwa Nnamdi Kanu

Kungiyar ta cigaba da caccakar shugaban kasa, inda tace duk da irin nakasun da shugaba Buhari yake da shi game da iya mulki, amma dai ya kamata akalla ace ya girmama kundin tsarin mulkin kasar da yake shugabanta.

A wani labarin kuma, Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB ya bayyana cewa har yanzu hukumar tsaro na sirri na rike da yan uwansa su 5. Kanu ya bayyana haka ne cikin wata wasika daya aika ma ministan kula da harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau da kuma shugaban hukumar kula da gidajen yari Ja’afaru Ahmed ta hannun lauyansa Ifeanyi Ejiofor, wanda jaridar Legit.ng ta samu kwafi, wasikar na dauke da kwanan wata 14 ga watan satumba, tare da shedar isarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel