Hamid Ali ya bayyana kan kokarin hukumar kastam

Hamid Ali ya bayyana kan kokarin hukumar kastam

–Wata babban kotun tarayya da ke zaune a jihar legas zata zantar da hukunci akan karan rashin hallacin kasancewan Hamid Ali a matsayin komtrola janar na Hukumar kastam

–Wani mai himmar aiki,Ebun-Olu Adegboruwa, ya kalubalanci nadin Hameed Ali akan cewan dole sai Wadanda suka kai matsayin mataimakin kontrola janar za'a iya baiwa matsayin komtrola janar.

Hamid Ali ya bayyana kan kokarin hukumar kastam

Rudani ya cika gari yayinda wata babban kotun tarayya da ke zaune a Legas ta sanya yau juma'a, 16 ga watan Satumba ranar zantar da hukuncin hallacin kasancewan Hammed Ali shugaban Hukumar kastam.

News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa Wani mai himmar aiki,Ebun-Olu Adegboruwa, ya shigar da karan gaban Jastis Sule Hassan a watan nuwamban 2015.

Mr. Adegboruwa wanda ya nemi kotu da ta warware nadin hammed Ali , ya nemi fassaran cewa shin shugaban kasa na da karfin nada duk wanda yaso a matsayin komtrola janar ba tare da bin dokar Section 3 of the Official Gazette ba.

Ebun-Olu Adegboruwa, ya kalubalanci nadin Hameed Ali akan cewan dole sai Wadanda suka kai matsayin mataimakin kontrola janar za'a iya baiwa matsayin komtrola janar.

KU KARANTA: Jami’an Kastam sun kama Bindiga da harsashai

Amma, Hukumar kastam ta shigar da karan kiyayya a ranan 29 ga watan afrilu tana kalubalantan hakkin wanda ya shigar da karan. Sun siffanta karan Mr. Adegboruwa a matsayin wasa kwakwalwa kawai wanda bai kamata kotu ta saurara ba. Kotu ta saurare su kuma ta dakatad da karan zuwa yau.

A bangare guda, tsohon shugaban kungiyan lauyoyin najeriya, Dr. Olisa Agbakoba, Ya baiwa shugaba Muhammadu buhari shawaran ya daina kukan kurciya, ya magance tabarbarewan tattalin arzikin kasa.

Dr. Olisa Agbakoba, ya bayyana hakan ne a wasikar da ya rubuta a ranan Alhamis,15 ga watan Satumba wanda kuma ya aika wa Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki da Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, akan rikicin tattalin arzikin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel