Durkushewar Tattali: Buhari na neman masu hannun jari

Durkushewar Tattali: Buhari na neman masu hannun jari

– Shugaba Muhammadu Buhari na neman hanyoyin tafiya da ‘Yan Kauswa masu hannun jari wajen shawo kan matsalar tattalin arzikin Kasar

– Shugaba Muhammadu Buhari na san ran cewa abubuwa za su yi kyau a bangaren

– Shugaban Kasan yace Gwamnatin sa za tayi amfani da halin da aka shiga domin kirkiro wasu damar

Durkushewar Tattali: Buhari na neman masu hannun jari

 

 

 

 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yace Gwamnatin sa za tayi kokarin kawo sauki ga ‘yan kasuwa a Kasar. Shugaban Kasar yace dole ayi tunanin yadda za a ceto Kasar daga halin da ake ciki na Matsalar tattalin arziki. Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi wannan jawabi ne jiya wajen taron da aka gudanar domin ceto tattalin arzikin Kasar.

A jiya Alhamis ne aka yi wani taro na kwana guda da Ministoci domin farfado da tattalin arzikin Kasar. Ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren Kasar ce dai ta shirya wannan taro a Garin Abuja. Shugaba Muhammadu Buhari yace matsalar da ake ciki na bukatar a tsaya ayi tunani kwarai, don haka ne ma Gwamnatin ta ke shirin tafiya da masu hannun jari. Hakan zai taimaka kwarai wajen gyara tattalin arzikin Kasar. Shugaban Kasar Muhammadu Buhari yana dai kuma sa rai cewa bangaren ‘Yan kasuwan zai yi kyau.

KU KARANTA: Ka sauka daga mulki, ba za ka iya ba-PDP tace da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Kasar yayi alkawarin kawo sauki wajen kasuwanaci a Najeriya. A cewar Shugaban Kasar, za ayi amfani da duk wani hali da aka shiga a Kasar domin kirkiro wasu damar cigaba musamman ga matasan mu. Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin Gwamnatin na samar da dama ta harkar wutar lantarki, gona, ICT na zamani, sufuri, kasuwanci da dai sauran su. Shugaba Muhammadu Buhari ya tunatar da matasa cewa Gwamnatin sa ba ta yi masu Kasa a gwiwa ba.

Shugaba Muhammadu Buhari na Kasar, yace Gwamnati ita kadai ba za ta iya ba. Ya zama dole masu hannun jari da ‘Yan kasuwar Kasashen waje su shigo ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel