PDP ta kara neman Shugaba Buhari ya sauka daga mulki

PDP ta kara neman Shugaba Buhari ya sauka daga mulki

- Jam'iyyar PDP tace Shugaba Buhari ya sauka daga mulkin Kasar

- Jam'iyyar PDP tace Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka, ya ba wadanda za su iya rike Kasar wuri

PDP ta kara neman Shugaba Buhari ya sauka daga mulki

 

 

 

 

 

 

Jam’iyyar adawar Kasar ta PDP ta kira Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki domin bada dama ga wadanda za su iya shawo kan matsalolin da Kasar ke fuskanta. Mai magana da bakin Jam'iyyar PDP ya fitar da wannan jawabi a jiya. Prince Dayo Adeyeye yace, ba zai yiwu a ciga da zurawa Jam’iyyar APC idanu ba.

Jam'iyyar PDP ta kira Buhari da ya maida Kasar yadda ya karbe ta a Mayun bara watau 2015. A cewar Jam'iyyar PDP, idan Buhari yayi hakan, sai ya tattara ya sauka daga mulkin Kasar inji PDP. Jam'iyyar PDP ta adawa ta Kasar  ta nuna damuwar ta ga yadda abubuwa suka tabarbare a Kasar. Jam'iyyar PDP ta bayyana yadda tattalin arzikin Kasar ya ruguje ciken lokaci kadan karkashin Minista Kemi Adeosun, wanda Jam'iyyar PDP ta kamanta da maras kishin Kasa kuma ba ta san aiki ba.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP kara sukar Shugaba Muhammadu Buhari

Jam'iyyar PDP ta kuma koka da yadda tattalin arzikin Kasar ya karye, kana ake kara samun rashin aikin yi a Kasa, da kuma yawan cin bashi. PDP tace har Kamfunan jiragen sama da bankuna, ba a bar su a baya ba, suna dakatar da aiki ko Koran ma’aikata a Kasar saboda yadda tattalin arzikin ya rushe. Jam'iyyar PDP tace a lokacin da ta ke Gwamnati, kowa ya san irin kokarin da tay a irin wadannan wurare.

Jam'iyyar PDPtace buhun Shinkafa yana N7000 lokacin da Buhari ya karbi Gwamnati, yanzu kuwa ya haura N20000. Tiyan wake ya tashi daga N150 zuwa N500. Ga kuma dalar Amurka ta kai N400 daga N197. Man fetur ma ya tashi, daga N87 zuwa N145 kowane lita guda.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel