Ku cigaba da goyon bayan Shugaba Buhari Inji Ministan Abuja

Ku cigaba da goyon bayan Shugaba Buhari Inji Ministan Abuja

– Malam Muhammad Musa Bello ya kira Inyamuran cikin Birnin Abuja da su cigaba da hada kai

– Ministan Birnin Tarayyar yace Shugaban Kasar na bukatar goyon bayan su domin ya cigaba

– Inyamuran sun ce kar a manta da su wajen cigaban Garin

Ku cigaba da goyon bayan Shugaba Buhari Inji Ministan Abuja

 

 

 

 

Ministan Babban Birnin Tarayya-Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya roki Inyamurai da ka da su janye goyon bayan su ga Shugaba Muhammadu Buhari. Ministan Abuja yayi wannan jawabi ne lokacin da Kungiyar Inymurai suka kai masa ziyara a Ranar Laraban nan. Ministan yace Shugaban Kasar Muhammadu Buhari, na bukatar goyon bayan da taimakon su domin ya kawo cigaba a Kasar.

Ministan ya kira Kungiyar Kabilar Inyamurai da su cigaba da marawa Shugaba Buhari baya, ba tare da duban yare ko kabila ba. Ministan ya kuma kira Inyamuran da su goyi bayan wadan da aka nada a Ma’aikatar Birnin Tarayyar domi kawo cigaba ga kowa a Babban Birnin. DailyPost ta rahoto Ministan yana cewa ba zai yiwu ayi maganar Abuja da cigaban da ta samu, ba tare da anyi maganar Inyamuran ‘Yan kasuwan da suka zauna a Yankin ba.

KU KARANTA: Shugaban Kungiyar ASUU ta Jami'ar Abuja yayi jawabi

Ministan ya kuma yi alkawarin kammala aikin jirgin Kasan Abuja zuwa karshen shekarar 2017, yayi kira da a zauna cikin hadin-kai da hakuri da juna a Garin na Abuja. Ministan ya nemi al’ummar cikin Garin da su taimakawa Jami’an tsaro da hadin kai da gwiwa wajen duk wani abu da ake bukata. Wani mai suna Eze Ibe Nwosu ne ya jagoranci tawagar Inyamuran, ya kuma yi alkawarin samun zama lafiya da juna.

Shugaban Tawagar, Eze Nwosu ya kuma nemi Ministan da ya gina sababbin kasuwanni, ya kuma gyara wadanda ke nan. Haka kuma ya tafi da Inyamurai cikin Ma’aikatan sa da sauran ayyuka, domin su san ana damawa da su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel