Muhimman labarun ranan Laraba

Muhimman labarun ranan Laraba

Jaridar NAIJ. com ta tattaro muku muhimman labarun da sukayi kani a ranan Laraba, 14 ga watan Satumba. Asha karatu

1.Bishap Kukah yace Buhari ya daina ganin laifin shugabanni magabata.

Muhimman labarun ranan Laraba

Shugaban cocin katolikan sokoto,Matthew Hassan Kukah, ya yi kira ga shugaba Buhari da fuskanci yadda zai farfado da tattalin arziki a maimakon ganin lsifin Wadanda suka gabata.

2.Maganan Okonjo Iweala ya tayar da kura.

Muhimman labarun ranan Laraba

Tsohuwar ministan kudi,, Dr. Ngozi Okonjo Iweala, ta kwace kanin labarai a yau bayan ya fito shirin ,The Stream a tashan yada labarai na Aljazeera inda tayi magana akan kalubalen najeriya. Maganan da tayi a shirin ya zama abun muhawara tsakanin yan najeriya a shafukan yanar gizo.

3. Wani fasto mai suna Caleb Sifuna, ya zube yayinda yake magana akan minbari.

Muhimman labarun ranan Laraba

Jaridar Tuko ta bada rahoton cewa Faston cocin Free Salvation Life Ministries da ke Kanduyi , Bungoma county ,ya fadi ne daga inda yake zaune gab da ya fara hudubarsa.

4. Tashin hankali a onitsha yayinda yan bindiga suka afka NTA.

Muhimman labarun ranan Laraba

Ma'aikatan gidan talabijin tarayya NTA a Onitsha ,Anambra sun ce yan bindiga sun kawo musu hari a jiya Laraba, 14 ga watan Satumba.

5. Boko haram sunyi barazanar kama Buhari a sabon bidiyo.

Muhimman labarun ranan Laraba

Bangaren boko haram sun saki sabuwar bidiyoda ke nuna dubunnan yan boko haram yayinda suke sallan idi. Kungiyar yan bindigan karkashin jagorancin.

Abubakar Shekau sun nuna mambobinsi a wurare 3 inda sukayi sallsn idi a batno da Chadi

6.Abubuwa 4 da ake sa ran Jonathan ya tattauna da Babangida.

Muhimman labarun ranan Laraba

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ys kai ziyara ga tsaffin shugabannin kasa,Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakr a minna, birnin jihar neja, Jaridar Punch ta lissafa abubuwan da sukayi yiwuwan tattaunawa a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel