'Yan Ijaw sun nemi gafarar sojoji

'Yan Ijaw sun nemi gafarar sojoji

Wasu matasan yankin kabilar Ijaw a yankin Niger Delta sun nemi gafarar sojojin Najeriya a bisa kisan wasu jikkata wasu daga cikin jami’anta

'Yan Ijaw sun nemi gafarar sojoji
Nigerian Army colours

Wata kungiyar matasan kabilar Ijaw IYC a yankin NigerDelta ta nemi gafarar rundunar sojin Najeriya a bisa jikkatar da wasu jami’anta suka  yi a yayin aiwatar da shirinta da ta yiwa lakabi da ‘Murmushin kada’.

A wani taro na manyan jami’an kungiyar na kasa a Fatakwal a ranar Laraba 14  ga wata Satumba, shugaban kungiyar na kasa, Elvis Donkemezou ya ce, ya zama doke kungiyar ta nemi gafarar rundunar sojin a kokarin da ta keyi na kawo karshen aikata manyan laifuka a yankin, musamman ta da kayar baya, da gwagwarmaya da makamai.

Shugaban kungiyar ya kuma yabawa babban hafsan sojin, Janar Buratai da kirkiro da shirin murmushin kada, wanda ya ce hakan zai rage yawaitar aikata manyan laifuka da kuma fashi a hanyoyin ruwa na yankin, shugaban kungiyar ya kuma tsame ‘yan kabilarsa daga aikata wadannan manyan laifuka yana mai cewa su masu zaman lafiya ne da ci gaban yakinsu da kuma kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel