Ana tuhumtar sojin Najeriya da cin mutuncin tsohuwa

Ana tuhumtar sojin Najeriya da cin mutuncin tsohuwa

Yan Najeriya sun yi ca ga rundunar sojin Najeriya akan fakewa da guzumar Operation Crocodile Smile suna harbin karsanar cin zarafin mutane.

Kungiyar Niger Delta Avengers sun tuhumci rundunar sojin najeriya da cin mutuncin masu manyan shekaru da matasa maras alhaki a yankin neja Delta.

Ana tuhumtar sojin Najeriya da cin mutuncin tsohuwa

Mutanen yankin neja delta sun fara nuna rashin yardarsu da Operation Crocodile Smile da aka kaddamar domin fitittikar yan bindigan yankin Neja Delta.

Amma, shugabannin sojin sun ce ba'a yi horon domin cin mutuncin kowa ba face kare su daga sharrin barayin mai . Amma an samu wata hitin da ysn kungiyar Niger Delta avengers suka saki na nuna yadda sojoji ke cin mutuncin wata mata a yankin neja delta.Sun watsa hoton ne suna cewa abinda sojoji suka iya shine cin zarafin tsaffin mata ,maza, da matasan yankin neja delta.

KU KARANTA: Ana tuhumtar Sojin Najeriya da cin mutuncin tsohuwa

Duk da cewan ba'a tabbatar da sihhancin hoton ba, wasu yan najeriya sun nuna bacin ransu game da abinda ake tuhumar sojin da shi. Amma wasu sunce frofaganda ce , hotunan Wadanda ke wurin ba sojojin Najeriya ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel