Wani dan Najeriya na nemi auren wata Baturiya

Wani dan Najeriya na nemi auren wata Baturiya

- An yada wani dan Najeriya saboda yadda ya nemi auren shi.                                                      

- Ya dauki budurwarshi baturiya zuwa Olumo rock in da ya nemi aurenta.

An yada wani dan Najeriya kan yadda ya nemi auren wata budurwarshi baturiya. Ya nemi aurenta a Olumo rock a garin Abeokuta, Najeriya.

Wani dan Najeriya na nemi auren wata Baturiya

Olumo rock wani wani sanannen gurin yawon bude ido ne wanda ya kayata birnin Abeokuta jahar Ogun, shine gurin da mutanen Egba suka boye lokacin yakin kabilu.

Mutumin ya tsara haka dan ya bata mamaki yayin yawon bude ido a Olumo rock, daga bangaren baturiyar kuma yadda mamaki ya cika ta, zamu iya cewa bata taba tsammanin irin wannan kaya taccen neman auren ba.

Wani dan Najeriya na nemi auren wata Baturiya

Bayan haka, munga abokan su suna yin hoto tare da su da taya su murna, haka ma masoyan da suka yadda da junansu, da yarjejeniyar aure sun sunbaci juna.

Wani dan Najeriya na nemi auren wata Baturiya

Wannan neman auren ya kayatar, muna taya su murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel