'Yan Najeriya ba Buhari shawara kan binciken Patience

'Yan Najeriya ba Buhari shawara kan binciken Patience

- Yayin da akema Patience Jonathan sabon zargi game da wasu kudi $20m, 'yan Najeriya sun fara mahawara koya dace gwamnatin Buhari ta binciki wanda ya gada da matarsa

- Inda wasu ke cewa ya kamata Buhari ya binciki duk wanda aka samu da hannu cikin cin rashawa, wasu kuma na cewa ba wani abu bane idan shugaba mai ci yana kashe kudaden da suka fi na wancan

'Yan Najeriya ba Buhari shawara kan binciken Patience

Zai iya kasancewa hukumar hana almundahana (EFCC) na binciken uwargidan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan kan zargin halarta kudin haram masu yawan $20m. Matar tsohon shugaban tayi ikrarin cewa asusunta ne bayan hukumar hana almundahana ta dakatarda asusun a cikin watan Yuli 2016 lokacinda ta kai wani ma'aikacin Jonathan  Waripamowei Dudafa, kara kan halarta kudin haram. EFCC tace da farko ba matar tsohon shugaban ake bincikeba amma da tace asusun nata ne, to akwai tambayoyin da zata amsa.

The Punch ta tambayi wasu sanannun 'yan Najeriya ko ya kamata gwamnatin tarayya ta binciki tsohon shugaba Jonathan da uwargidansa Patience kan $20m.

Yusuf Ali (Babban Lauyan Najeriya) yace: "A ganina gwamnati na iya binciken kowa. A nawa ra'ayin binciken tsohon shugaba Goodluck Jonathan, da uwargidansa, Patience, ba wani abu bane in dai zasu iya kare kansu, in kuma ba haka ba to abar doka tayi aikinta. Duk lokacin da gwamnatin ke zargin wani, to ya kamata a gayyaceshi domin amsa tambayoyi".

KU KARANTA:Muhimman labarun ranan talata

Osita Ogbu (Shaihin malamin shari'a/Daraktan cibiyar habaka damokradiyya da shari'a): “Baya ga miliyoyin daloli da aka alakanta da Patience Jonathan, gwamnatin tarayya nada hurumin ta binciki ko wanene. Zargi kadai ya isa a binciki Mrs. Jonathan kamar kowa balle ga shedar samunfa da makudan kudade da akayi. Samun Jonathan da matarsa da asusun kasar waje ya isa yasa a bincikesu. Yayin mulkinsa an kara ma Mrs. Jonathan girma zuwa babban sakatare, wanda shine mukami mafi girma da ta rike. Nawa ne albashinta in an tara shi duka? Ina ta samu wadannan kudaden? Shin ta bayyana kaddarorinta lokacin da aka zabi maigidanta shugaban kasa?"

Auwal Musa (Shugaban, Amnesty International, a Najeriya) ya fadi ra'ayinsa: "Duk wanda aka kama da kudin zargi, ya kamata yayi bayanin asalin kudin. A wannan anyi daidaitoni kudin na Mrs. Jonathan ne. Abinda ke da muhimmanci shine ayi cikakken bincike na asalin kudin, da lokacin da aka sasu cikin asusun, idan matar tsohon shugaban ta bada jawabin daya gamsarda jami'an tsaro, ba wani abu a ciki"

Asali: Legit.ng

Online view pixel