Dan sanda da Karya doka ya janyo ka-ce-na–ce

Dan sanda da Karya doka ya janyo ka-ce-na–ce

Wani dan sanda ya kwashi dambe da wani mai tuka mashin mai kafa uku da ake kira keke Napep ko a daidaita, wanda hakan ya janyo ka-ce-na-ce

Wannan abu mai kama da almara ya faru ne a cewar wani ganau, a kan titin Oron da ke Uyo,  babban birnin jihar Akwa Ibom a ranar Asabar 12 ga watan Satumba.

Dan sanda da Karya doka ya janyo ka-ce-na–ce
Dan sanda da matukin keke mai kafa uku na dambe a kan titi

A cewar wanda ya shaida lamarin, wanda kuma ya samu damar daukar hotunan dan sandan da kuma abokin fadan nasa, ya ce, dan sandan ne ya yi tsalle ya shiga keken mai kafa uku a kokarinsa na tsayar da mashin din da karfin tuwo.

Dan sanda da Karya doka ya janyo ka-ce-na–ce
Mashin mai kafa uku da ake zargin Dan sanda ya haddasa hadarinsa da karfin tuwo a Uyo

Sannan ya kuma ci gaba da cewa, Dan sandan ya rike kan mashin din a inda suka shiga kokawa da matukin da hakan ta kai mashin din ya fadi, wanda kuma hakan ya sa fasinjojin ciki suka samu munanan raunuka a inda wasu suka rika zubar da jini a wurin, a cewarsa.

Bayan faduwar mashin din, Dan sanda da kuma mai mashin suka cakumi juna, a inda kowa ya rike wandon dan uwansa a inda mutane suka kewayesu suna kallo.

An samu irin wannan a jihar Lagos a inda wasu jami’an kare kiyayye hadari FRSC suka haddasa wani hadari a wata mahada a jihar, a inda jama’a suka fusata har suka yi musu dukan kawo wuka, a jihar Kano ma hakan ta taba faruwa da inda wani jami’in kiyaye haddura na KAROTA ya yi kokarin tsayar da wata motar fasinja da karfin tuwo, ya haifar da haddari a kan titin zuwa Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel