Wata Kungiya ta zargi Buhari da karya hakkin Bil-Adama

Wata Kungiya ta zargi Buhari da karya hakkin Bil-Adama

– Wata Kungiya mai suna ‘Opinion Nigeria’ ta rubuta takarda ga taron Majalisar dinkin duniya inda ta zargi Shugaba da karya dokar hakkin ‘Yan Kasa

– Kungiyar ta nemi Majalisar dinkin duniyar da ta sa baki cikin abin da ke faruwa a Kasar, karkashin mulkin Shugaba Buhari

– Wannan Kungiya tace Gwamnatin APC ta saba tauye hakkin Bil-Adama a Kasar

Wata Kungiya ta zargi Buhari da karya hakkin Bil-Adama

 

 

 

 

Wata Kungiya mai suna ‘Opinion Nigeria’ da ke Garin Abuja ta rubuta takarda ga Majalisar dinkin duniya inda ta zargi Shugaba da karya dokar hakkin ‘Bil-Adama a Kasar Najeriya. Kungiyar dai ta rubuta wannan takardar ne daidai lokacin da ake shirin taron Majalisar dinkin duniyar karo na 71 a Birnin New-York da ke Amurka. Vanguard ta rahoto cewa an rubuta wannan takarda ne ga Michel Forst, wanda ke kula da hakkin kare mutuncin Bil-Adama a Majalisar.

Kungiyar ta OPINION NIGERIA da wani Jeff Okoroafor yake Shugabanta dai tayi kira da Majalisar ta dinkin Duniya da ta ceci Najeriya daga kece hakkin Bil-Adama karkashin Shugabancin Muhammadu Buhari. Kungiyar ta zargi Shugaban Kasar da halin ko-in-kula da ko-oho game da wasu sha’anin Kasar.

KU KARANTA: Buhun shinkafa zai zama N40000 idan ba ayi noma ba-Minista

Cikin laifuffukan da suka lissafa dai akwai zargin kashe mutane fiye da 100 da Hukumar JTF tayi lokacin zaben Jihar Rivers, sannan kuma Jami’an ‘Yan sanda sun tare masu zanga-zangar nan ta #BringBackOurGirls, bayan da Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda ya haramta zanga-zangar. A ranar 6 ga Watan Satumba. Haka kuma dai tana zargin Gwamnatin Shugaba Buhari da kisan gilla ga ‘yan Kungiyar IPOB na Biafra a karshe watan Mayu. Kungiyar ta kuma bayyana yadda Sojin Kasar suka yi wa ‘Yan Kungiyar ‘Islamic Movement of Nigeria’ IMN kisan kare dangi a Zaria.

Kungiyar ta kuma zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da cigaba da garkame Nnamdi Kanu na Biafra da kuma kyale Fulani suna kashe mutane a Kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel