Kamfanin Jirgin Arik sun dakatar da aiki a Najeriya

Kamfanin Jirgin Arik sun dakatar da aiki a Najeriya

- Kamfanin Jirgi na Arik Air sun dakatar da aiki a Najeriya da fadin Yammacin Afrika saboda tulin bashin da masu mai ke bin su

- Mutane da dama dai sun makale cirko-cirko a Najeriya dalilin rashin tashin jirgin a Kasar

Kamfanin Jirgin Arik sun dakatar da aiki a Najeriya

 

 

 

 

Jirgin Arik ya dakatar da aikace-aikacen sa a Najeriya da Afrika saboda wasu dalilai na sake takardun inshora. Mai magana da yawun-bakin Kamfanin, Mista Adebanji Ola ya bayyana haka a Jiya. Mista Ola yace an dakatar da duk wata tafiya saboda rashin sabunta takardu.

Mutanen Kasar dai tuni suka fara ce-ce-ku-ce game da wannan batu, inda suka tambaya anya wannne shine canjin da Shugaba Buhari yake nufi, ko kuwa dai ya ya? Kadan daga cikin abubuwan da wasu ke fada a shafin twitter:

KU KARANTA: UN za ta agazawa Kasar Najeriya

Wani yace; To kun ji! Kamfanin Jirgin Arik fa sun dakatar da aiki, saboda rashin kudi a Gwamnatin Canji!

Wani yace to wani ina ruwan sa da Jirgin Arik tun da motar dare yake hawa a tasha.

Wani kuma kokawa yayi da yadda mutane ke rasa ayyukan su a Kasar. Yace kuma ace daga gare sa za a fara samun canji?

A cewar wani idan dai har Arik sun tsaida aiki, sai a rufe tashoshin jiragen.

Wani kuwa yana jin labarin sai yace Sai Buhari!

Buhari dai so yake mu kashe dalololin mu a nan, mu tafi Amurka a titi… Inji wani dan Kasar.

Wani mai shirin zama Ango yace, an daga aure na, gas hi Arik sun daga aiki! To ni ya za ayi da kudi na?

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel