Babu maganar zuwa yajin aiki-Inji Kungiyar ASUU

Babu maganar zuwa yajin aiki-Inji Kungiyar ASUU

– Shugaban Kungiyar ASUU ta cibiyar Jami’ar Abuja ya musanya batun tafiyar su yajin aiki kwanan nan

– Dr Ben Ugheoke da ke Jami’ar Abuja yace duk rade-raden karya ne kurum

- Shugaban Kungiyar ya bayyana cewa ba a yi wata hira da shi ba a baya

Babu maganar zuwa yajin aiki-Inji Kungiyar ASUU

 

 

 

Dr Ben Ugheoke wani Shugaban Kungiyar ASUU ta cibiyar Jami’ar Abuja yace babu maganar shiga yajin aiki a Ranar 2 ga watan Oktoba. Shugaban Kungiyar ta Malaman Jami’o’i na Kasa yace rade-raden banza ne kawai ake ta yadawa cewa Kungiyar Malaman za su shiga wani yajin aiki wata mai zuwa

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Dr Ugheoke ya bayyana ma ta cewa Kungiyar ASUU ba ta sanar da Gwamnatin Tarayya wani shirin tafiya yajin aiki ba. Shugaban Kungiyar ASUU ta Bangaren Jami’ar Abuja ya kuma tabbatar da cewa babu wata hira da aka yi da shi ba a baya inda ya bayyana cewa za su tafi wani yajin aiki a cikin watan Oktoban gobe. Yace bai tattauna da wani ba, ko ya kai ga bada jawabi game da shirin zuwa yajin aiki.

KU KARANTA: Muna bin Gwamnati bashin kudi-Kamfanin wuta

Dr. Ugheoke yake magana game da rahotannin da aka yi ta yadawa a kafafe cewa ASUU za ta shiga yajin aiki a Ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa. Yace:

‘Labari ya kai gare ni cewa wai Kungiyar ASUU za ta tafi yajin aiki a Ranar 2 ga watan Oktoba….Babu wani dan jarida da ya zo uwi na muka kuma tattauna hakan, don haka na ke tabbatar da cewa wannan sako da aka gani a baya, ba gaskiya bane. ASUU ta san wannan, ban yi hira da kowa ba, inda na fadi hakan’

Dr. Ugheoke ya kara da cewa, ASUU ba wannan bace gwagwarmayar da ASUU take yi, burin ta a gyara harkar ilmi a Kasar nan. Ya kira jam’a su san cewa ba shi y fadi wancan labari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel