Ku godewa Allah; Shine sakon Buhari ga 'yan Najeriya

Ku godewa Allah; Shine sakon Buhari ga 'yan Najeriya

Shugaba Muhammad Buhari wanda yayi sallah a garinsa Daura dake jihar Katsina ya kira jama'ar Najeriya da su godewa Allah saboda ya arbarkaci kasar da damina mai kyau kuma ayyukan da gwamnati ta sa a gaba na cigaba kama daga yaki da cin hanci da rashawa zuwa samarda wutar lantarki.

Yayinda 'yan Najeriya suka yi babbar salla a hali daban daban, wasu sun yi yanka wasu kuma basu samu sun yi ba, shi kuwa shugaban kasa a garinsa ya yi.

Bayan ya kammala Idi da kuma yanka da yayi a gidansas hugaban ya aikawa 'yan Najeriya da sako da ya shafi yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa ta sa gaba akai..

Shugaban yace wanda Mu godewa Allah damina tayi albarka. Mutane su fahimci halin da muka samu kasarmu...Shekara goma sha shida da waccan jam'iyya da gwamnatoci guda takwas, da muka zo muka tambaya ko an yi tanadin wani abu babu.

Yaya batun lantarki? da kowa ke bukata babu. Babu dogo, jirgin kasa. Babu hanyoyin mota. Babu sha'anin tsaro. Saboda haka muka ce to me aka yi da kudin? Babu wanda ya bamu amsa amma mun fara kama wadanda suka san yadda aka yi da kudin. Saboda haka mutane su godewa Allah. Boko Haram mun san yadda muka yi dasu. Su ma na Niger Delta zamu san yadda muka yi dasu.

Ya cigaba da cewa wanda Mun godewa Allah ya bamu damina mai albarka.... Su kara ba gwamnati goyon baya.... Zamu yiwa mutane adalci kuma wadanda suka zalunci kasa , ba za'a yiwa kowa sharri ba amma duk wanda aka samu yayi sata za'a ce ya maido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel