Wani dan jarida ya bata

Wani dan jarida ya bata

Wani dan Jarida, mawallafin mujallar The Vigilante da kuma Sintiri ya yi batar dabo kan hanyarsa ta zuwa Abuja gudanar da aiki

Wani dan jarida ya bata
Adamu Isah tsohon dan wasan kwaikwayo ne kuma dan jarida mai zaman kansa, shi ne mawallafin mujallar Vigilante da kuma Sintiri

Wani dan jarida mai zaman kansa ya yi batar dabo a yayin da ya bar ofishinsa a safiyar ranar Lahadi don zuwa Abuja wajen yin hira da wani babban mutum.

Dan jaridar mai suna Adamu Isah mawallafin mujallar turanci mai suna The Vigilante da kuma Sintiri, a cewar wata sanarwa da abokan aikinsa suka lika a dandalin sada zumuta da muhawara na Facebook, ta ce, ya bar ofishinsa da ke SKY shopping Complex ne a titin Zoo road a safiyar ranar Lahadi 4 ga watan Satumba.

Adamu Isah ya zo da jakarsa a inda ya bar wa mai gadi da umarnin cewa, shi ya yi gaba, ba zai iya jira ba, kuma idan abokin aikinsa ya zo, wanda da shi za su yi tafiyar, ya taho masa da ita. Ana tunanin ya yi hakan ne domin ya isa Abuja da wuri a motar haya, ya kuma samu wanda za su yi hirar da shi kan lokaci, kar ya kubuce.

Amma da barinsa wurin da kimanin minti 15, da aka nemi shi a waya sai aka rasa, kuma tun daga ranar har zuwa yanzu, babu wanda ya gan shi ko ya ji labarinsa, ana zaton ko ya shiga kananan motocin haya da ke kan shatale-talen Dangi ne masu asubancin daukar fasinjoji zuwa Kaduna da Abuja.

Babban kwamandan kungiyar Vigilante ta kasa, Usman Mohammamed Jahun kuma na hannun daman Adamu Isah ya tabbatar da labarin, ya kuma da kara da cewa, har yanzu babu labarinsa.

A ‘yan kwankin nan Hukumar Kula da ababen hawa da bin ka’idojin hanya ta jihar Kano KAROTA, ta dage da fadakarwa kan shiga motocin haya a gefen titi a maimakon shiga tasha, saboda gujewa fadawa hannun bata gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel