Dan majalisa ya raba raguna 100, da buhun shinkafa 500

Dan majalisa ya raba raguna 100, da buhun shinkafa 500

Duk da irin halin matsi da ake ciki, Yarima Muhammad Idris Ndako yayi hubbasa wajen rage ma al’ummarsa radadin lalacewar tattalin arziki a lokacin bikin babbar Sallah.

Dan majalisa ya raba raguna 100, da buhun shinkafa 500
Muhammad Ndako

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Lokoja 11 a majalisar jihar Kogi Yarima Muhammad Ndako ya raba ma al’ummar mazabarsa raguna 100 da buhuhunan shinkafa 500 a ranar asabar 10 ga watan satumba. A yayin rabon, dan majalisar ya bayyana kayayyakin a matsayin tallafi ga masu karamin karfi, sa’annan ya musanta alakar kyautan da jita jitan takarar majalisar wakilai da ake yi masa.

Ya bayyana cewa manufar sa shi ne bauta ma al’ummar mazabarsa yadda ya kamata, tare da cika alkawarin daya daukan musu yayin yakin neman zaben shekara ta 2015. Ndako wanda shi ne shugaban al’aummar Felele ya bayyana haka ne a wajen raba kayayyakin, yace “wasu jama’a suna cewa wai ina amfani da wannan damar ne don neman tsayawa takarar dan majalisa wakilai a 2019. Gaskiya a yanzu, damuwana shi ne in ga na na taimaka mazabata yadda ya kamata, tare da cika alkawarin dana daukan musu yayin yakin neman zaben shekara ta 2015. Ba zaka iya hana mutane fadin ra’ayinsu ba, amma a yanzu bukatata shi ne in faranta musu rai.”

KU KARANTA:Idin Babbar Sallah: Masu raguna sun koka da rashin kasuwa

A yayin bayar da tallafin, dan majalisan ya bayyana cewa ya raba kayayyakin da suka haura darajat naira miliyan 5 a watan Ramadan. “a cikin kwanaki 28 da suka gabata, nayi amfani da daman a wajen ciyar da talakwa a gaba daya mazabu 5 dake karkashin mazabata. A yanzu ma nazo in raba muku raguna 100, da buhun shinkafa 500 don gudanar da bikin Sallah.

“Nufi na na bayar da tallafin nan shi ne don cika alkawarin da nayi na ciyar da jama’a na, tare da tabbatar da ganin sun gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki da annushuwa.” Ndako yace.

AH wani labarin kuma, gwamnatin jihar Sakkwato tayi hubbasan ganin ta faranta ma marayu rai a jihar a yayin bikin babbar Sallah. Kamfanin dillarcin labarai (NAN) ta ruwaito gwamnatin jihar Sakkwato ta bada umarnin a sayo ma marayun shanu na naira miliyan 11 don ciyar da marayu 4,205, kamar yadda shugaban kwamitin zakka na jihar Alh Lawal Maidoki ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel