Sallah: Shugaban CAN ya mika sakon taya murna ga musulmai

Sallah: Shugaban CAN ya mika sakon taya murna ga musulmai

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) rabaren Samson Ayokunle ya bukaci yan Najeriya dasu kawar da kiyayya ta hanyar rungumar juna da nuna kauna da zaman lafiya, musamman a wannan lokacin bikin babbar Sallah na ranar 12 ga watan Satumba.

Sallah: Shugaban CAN ya mika sakon taya murna ga musulmai
Rabaren Samson Ayokunle

Sa’annan cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a birnin Abuja, ya taya musulman kasar nan murnar gudanar da babbar Sallar bana.

Jaridar Vanguard ta ruwaito shugaban CAN yana addu’ar ina fatan murnan babbar Sallah ya dawwama tare daku, da fatan muhimmancin bikin zai sanya dankon zumunci a tsakanin mu gaba daya, tare da samar da zaman lafiya da cigaban kasa gaba daya.

Duk da cewa muna cikin wani matsanancin hali na lalacewar tattalin arziki a Najeriya, amma ya zaman dole mu gamsu cewa Ubangijin daya baiwa Annabi Ibrahim rago a cikin sahara,zai kawo mana sauki ta hanyar biya mana bukatun mu, a yanzu da gaba.

KU KARANTA:Kungiyar CAN ta samu sabon shugaba.

Rabaren Samson ya cigaba da addu’ar wanda idan ma baku samu daman gudanar da bikin ba yadda ya kamata sakamakon karancin abin hannu, toh ku zauna da tabbacin sallar badi zata fi haka kyau. Ina kira da mu dage da yima kasar mu addu’a daurewar zaman lafiya, hadin kai da cigabar kasa, sa’annan muyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnatinsa addu’ar Allah yayi musu jagora.

Daga karshe, Rabaren Samson ya karkare da cewa muyi amfani da wannan lokacin don nuna soyayya ga juna, kuma mu zauna lafiya da juna.da fatan zamu samu cigaban da kowa zai amfana a kasar mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel