Ministan mata ta maganta kan Chibok

Ministan mata ta maganta kan Chibok

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa 'yan mata biyar daga cikin 'yan Matan Chibok 10 da aka kai Amurka da sunan karatu, an yaudare su ne inda aka yi amfani da su wajen neman kudi a kasar.

Ministan Harkokin Mata, Aisha Alhassan ce ta tabbatar da haka inda ta nuna cewa 'yan Matan na cikin wadanda suka fara tsirewa daga hannun mayakan Boko Haram a lokacin da suke kokarin arcewa da su.

Ta ce, a wancan lokacin wasu kungiyoyi sun tuntubi iyayen 'yan Matan da nufin taiamaka masu da guraban karo ilimi a Amurka amma bayan sun tsallaka da su, sai su ki saka su Makaranta a maimakon haka aka yi amfani da su wajen biyan wata bukata na daban.

Ta kara da cewa Shugaba Buhari ne ya umarce ta kan ta yi bincike kan zargin inda ta nesanta gwamnati da hannu cikin badakalar tana mai cewa iyayen Matan ba su sanar da gwamnati ba kafin su bari a tsallaka da 'ya'yansu zuwa Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel