An sace da shanu da Fulani

An sace da shanu da Fulani

Rahotanni daga Enugu sun tabbatar da cewa kimanin shanu 100 ne aka arce da su bayan wani sabon rikici da ya barke tsakanin manona da makiyaya a jihar.

Rikicin dai ya faru ne a karamar hukumar Igbo-Etiti inda aka raunana wani Fulani guda yayin da kuma wasu mutum biyu suka bace. Wanda al'amarin ya shafa, Alhaji Sodu ya bayyana cewa matasan yankin Aku ne suka kai masu harin inda suka kuma yanka shanu bakwai kafin sun arce da guda 100.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel