Yaro na,da shanaye 100 sun bace – Fulani Makiyayi

Yaro na,da shanaye 100 sun bace – Fulani Makiyayi

–Wani Fulani makiyayi yayi ikirarin cewa daya daga cikin yaransa ya bace,kuma daya yaji rauni

–Yana kira ga jami’an tsaro da su taimaka su ceto yaransa kuma su kama barayin

Yaro na,da shanaye 100 sun bace – Fulani Makiyayi

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa,bayan wani hari da aka kaima Fulani makiyaya a jihar Enugu,shanaye 100 sun bace. Wani makiyayi mai suna Alhaji Sodu  ace harda yaronsa aka sace

Alhaji Sodu yanada imanin cewa matasan unguwar Aku a karamar hukumar  Igbo-Etiti ne suka kawo musu harin da shi ya raunana a wurare 3 da harsashi ,kuma wasu guda 3 ma sun raunan,yaronsa daya ya bace.

Yaronsa da ya ji rauni sunansa Wareri amma Musa,Buba da Muhammadu ne mutanen da suka bace yayinda matasan unguwar Attaukwu a karamar hukumar Nkanu-West suka kawo harin ramuwar gayya akan kisan wani fasto lazarus Nwafor. Ana sa ran Wareri zai rayu yayinda aka kai ziyara asibiti amma mahaifin yace jami’an tsaron su tabbatar da cewa an kama masu laifin.

“Na tsufa da in shiga cikin daji neman yarana. Ina kira ga jami’an tsaro su ceto mini yara na. matasan sun yankan mini shanaye 3 kuma sun sace 100.

KU KARANTA KUMA:Anyi zanga-zanga a jihar Akwa Ibom kan harin makiyaya

Jami’in soja Brigadier General Fred Eze ya nada wata kwamiti kuma yac za’a kwantar da kuran . yace : “Muna nuna damuwan mu da al’amarin,rundunar soji zasu tabbatar da doka. Kwamanda O.T Akinjobi ya tura wasu soji su nemo yaran. Wata tawagar jami’an soji da yan sanda sun shiga unguwar domin tabatar da zaman lafiya. Ana gudanar da bincike kan al’amarin. Za’a gano dalilan kuma a dau mataki da ya kamata.

A bangare guda, wasu mata manoma 3,000 sun yi zanga-zanga akan ayyukan Fulani makiyaya a yankin kudu maso gabas.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa manyan mata yan unguwar Ishiagu sunyi zanga-zanga zzuwa fadan sarkin su HRH Ezego Moses Ngele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel