Mai ‘yaya maza 13 ta lashi takobi sai ta haifi ‘ya mace

Mai ‘yaya maza 13 ta lashi takobi sai ta haifi ‘ya mace

–Irineu Cruz da Jucicleide Silva ma’aurata ne a kasar Brazil

–Shekaran su 20 da aure kuma sun haif yara maza goma sha uku

–Jucicleide Silva tace ba zata daina haihuwa ba sai ta haifi ‘ya mace

Mai ‘yaya maza 13 ta lashi takobi sai ta haifi ‘ya mace

Irineu Cruz ,wani manomi dan shekara 40 da matarsa Jucicleide Silva ma’aurata ne a kasar Brazil. Sun kasance suna haihuwa yara maza kuma har yanzu basu samu ‘ya mace ba. Sunyi shekara 20 suna neman haihuwan ‘ya mace.

Sunyi alkawarin cewa idan ta haifi namiji,mijin ne zai baiwa yaron suna ,hakazalika idan ta haifi mace, matar ce zata sa ma yarinyan suna, amma har yanzu bata samu ‘ya mace ba.

Irineu Cruz ya sanya ma yaronsa maza sunayen shararrun ‘yan kwallo kuma yace : “Na kasance ina ‘yan kwallo Kaman Rivaldo da Ronaldinho, na lura cewa duka sunayensu ya fara da ‘R’ saboda haka na sanya musu sunan.

KU KARANTA KUMA:Yunwa da cututtuka na hallaka ‘yan gudun hijira –Rahoton MSF

Jucicleide ta lashi takobin ba zata daina hayayyafa ba sai ta haifi ‘ya mace

Ga sunayen yaran da shekarunsu Robson (18), Reinan (17), Rauan (15), Rubens (14), Rivaldo (13), Ruan (12), Ramon (10), Rincon (9), Riquelme (7), Ramires (5), Railson (3), Rafael (2) and Ronaldo, (wata 1).

Asali: Legit.ng

Online view pixel