Nakasashen Dan Najeriya Ezuruike ya ci zinariya a Rio

Nakasashen Dan Najeriya Ezuruike ya ci zinariya a Rio

Bayan wata nakasashiyar yar najeriya Latifat Tijani ta ci azurfa a gasar wasan cin karfe a Rio Paralympics, wani dan najeriya ya keta tarihi ya ciyo ma najeriya zinariya.

Nakasashen Dan Najeriya Ezuruike ya ci zinariya a Rio
Nigeria's Ezuruike

Rahotanni sun nuna cewa Roland Ezuruike Yaci gasar cin karfen kilo 54 ,kana ya keta tarihi na samun kilo 190 wanda ya ciyo ma najeriya zinariyarta na farko a gasar da ake yi a Brazil. Roland Ezuruike ne ya fara keta tarihi a duniya kuma ya sake keta wani tarihin a wannan shekaran.

KU KARANTA KUMA:Nigeria ta ci Tagulla a gasar Nakasassu ta duniya

Bayan Latifat ya fadi da kiris a gasan matan kilo 45 wanda wata yar kasar sin ne taci, da najeriya ta samu zinariya 2 yanzu.

Ana sa ran nakasassun yan wasan zasu ciyo kyaututtuka wasan cin karfe saboda shine wasan da yan najeriya suka keta raini a gasar Olympics na nakassasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel