Anyi shirin jibge sojoji 10,000 a Neja Delta

Anyi shirin jibge sojoji 10,000 a Neja Delta

– Lt Gen Tukur Buratai yace ya zuwa 2017 za'a jibge sojoji 10,000 a Neja Delta

-Yace a halin yanzu an kai sojoji 3,000 a yankin

-Gwamna Dickson ya bukaci sojoji subi hanyar lalama wanen yaki da masu karya doka a yankin

Anyi shirin jibge sojoji 10,000 a Neja Delta

Shugaban sojojin kasa Lt. Gen. Tukur Buratai, ya fada cewa za'a jibge sojoji 10,000 a yankin Neja Delta ya zuwa 2017, a cewar rohoton The Punch. Yace, a halin yanzu an kai sojoji 3,000 domin samamen da suke kaiwa mai suna 'Operation Crocodile Smile’ a yankin. Ya fadi haka lokacin daya kai ziyarar ban girma ga gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa, a gidan gwamnati dake Yenagoa ranar Alhamis 8 ga Satumba. Yana kuma tabbatarma mutanen yankin cewa samamen da sojojin keyi domin tsaronsu ne, kuma sojojin nada ka'idojinsu na yaki.

KU KARANTA KUMA:Dattawa da matasan Neja Delta sun fadi bukatunsu ga Buhari

Yayin da yake maida martani, gwamna Dickson yana yabama sojojin domin sadaukar da kansu wajen aikinsu. Ya kuma Jajantama sojojin rashin wasu sojoji da akayi cikin wani hadarin kwace-kwale da akayi cikin jihar, ya kuma bukaci sojojin dasu bi hanyar lalama wajen kawo karshen tsageranci a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel