An kona mutum da ransa

An kona mutum da ransa

 A garin Ikot Epekne, jahar Akwa Ibom, an kona wani mutum da ransa saboda zargin da ake mai na satar mashin (acaba) ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba.

Mai makon su mika barawon mashin din zuwa ga yan sanda, wasu fusatattun taron mutane, wadanda yawan ci yan acaba ne, suka dauki doka a hannun su in da suka yi ta dukan mutumin ba tausayi, ba su tsaya a nan ba sai suka hada tayoyi , suka saka mutumin a ciki suka watsa mai kalanzir sai suka kunna mai wuta.

An kona mutum da ransa
An kona mutum da ransa

Abin mamaki a nan shine dan me har yanzu mutane ke daukar doka a hannun su, mai makon kai kara ga yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel