An kama ta da akwatin gawa cike da matattun yara a mota

An kama ta da akwatin gawa cike da matattun yara a mota

An kama wata mata dauke da akwatin cike da gawar wasu kananan yara a motar ta.

Kamar yadda wata yar fim Diora Chidera-Adiele za rubuta a shafinta na facebook tace an kama matar ne yayin da take tuka motar ta kirar SUV kan hanyar Mowe/Ibafo a jihar Legas, bayan gudanar da binciken kwakwaf, sai aka gano gawar kananan yara su 6 (uku maza, uku mata) an fille kawunansu, a bangaren ajiye kaya na motar.

Ga yadda ta rubuta labarin

Barkan ku da yini, gaskiya na rasa irin halin da duniyar mu take ciki. A jiya ne yansanda suka kama wata mata tare da direban ta a kan hanyar Berger/Ibafo, a cikin motar akwai akwatin gawa, sai dai taki bari a bincika a gani, sai ta dinga ma yansanda ihu, tana kokarin yin fada dasu, inda take fada musu wai gawar mijinta ne.

Saura kiris yansandan su aminta da ita, amma sai daya daga cikinsu yaje ya bude wajen ajiyan kayan motan, inda ya bude akwatin gawar.

KU KARANTA: Dan shekara 50 ya kashe yarsa bayan ya mata ciki

Budewarsa keda wuya, sai ga gawar kananan yara guda 6, 3 maza da gangan jiki 3 na mata ba kai, da kuma hanjin mutane da dama daure cikin takarda.

Kuma matar na hanyar fita daga jihar Legas ne, ina da tabbacin wannan shine kasuwancin ta. Allah ya kona ta wuta. Jama’a mu kula da yayanmu, da ma wadanda ba namu ba, musa ido domin miyagun mutane sun yawaita a duniya. Allah ya jikan rayukan yaran da aka kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel