Hukumar kare haddura zata tilasta amfani da na’urar rage gudu

Hukumar kare haddura zata tilasta amfani da na’urar rage gudu

Hukumar kare haddura ta kasa (FRSC) ta gargadi direbobi masu tsananin gudu da mota a kan hanyoyi cewa zata sa wando daya da duk wanda aka kama daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Hukumar tace zata fara tilasta amfani da na’urar kayyade gudu a dukkanin fadin kasar nan.

Hukumar kare haddura zata tilasta amfani da na’urar rage gudu
Shugaban hukumar FRSC Boboye Oyeyemi

Shugaban hukumar FRSC Boboye Oyeyemi ya bukaci matuka mota a kasar nan dasu daura ma motocinsu na’urar kayyade gudu. Jaridar Punch ta ruwaito Boboye yana cewa ya gargadi direbobin haya daga kauce wa karya umarninsu.

Oyeyemi ya bayyana haka ne a wani taron wayar da kan al’umma daya gudana a ranar Laraba a garin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda ya bayyana cewa an tsayar da ranar ne don rage yawan mace mace a kan hanyoyin kasar nan, musamman a watannin karshen shekara lokacin da aka fi samun haddura.

“Za’a iya magance duk hadduran dake faruwa a kasar nan, idan zamu iya rage gudu a ababen hawa, da haka ne zamu iya rage mace macen rayuka a kan hanyoyin mu,” in ji shi.

Oyeyemi ya samu wakilcin mataimakinsa Michael Olagunju ya bayyana yawan hadduran dake faruwa a kasar a matsayin abin ban tsoro, kuma yafi karfin hankali.

KU KARANTA:Mummunan hatsari ya auku a hanyar Bauchi zuwa Kano

Kwamishinan sufuri na jihar Akwa Ibom Godwin Ntukude ya yaba da kokarin hukumar na kirkiran na’urar kayyade gudu, sai ya bukaci hukumar data kara wayar da kan direbobi.

“Babu wani tsari da gwamnati zata fitar da shi ba tare da ya amfani jama’a ba, amma ya kamata a gayyato masana da kwararru don su duba yiwuar sanya na’urar akan gwanjon motoci,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel