Ekweremadu ya roki Buhari da ya dena muzguna ma yan jam'iyar PDP

Ekweremadu ya roki Buhari da ya dena muzguna ma yan jam'iyar PDP

- Mukaddashin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremedu ya bayyana damuwarsa                                                        

- Kamar yadda yan jam'iyar PDP na Edo suka bayyana an fara muzguna masu kafin zabe mai zuwa da za'ayi na gwamna a jahar ranar Asabar                                        

- Ekweremadu ya roki shugaban kasa Buhari da ya saka baki kuma ya tabbatar anyi zabe mai tsafta ba magudi.

Mambobi kuma magoya bayan jam'iyar people democratic party (PDP) na reshen jahar Edo sun koka cewa hukumomin tsaro suna muzguna masu a cikin jahar.

Wannan bayanin ya zo maku ne daga mukaddashin majalisar dattawa Ike Ekweremedu, wanda ya biyo hannun mai bashi shawara kan sha'anin sadarwa Uche Anichukwu ranar Laraba.

Ekweremadu ya roki Buhari da ya dena muzguna ma yan jam'iyar PDP
Mukaddashin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu

Yace wanda nayi matukar takaicin haka ba dan kasancewa ta dan PDP ba, amma abunda yafi amfani shine, jam'iyar PDP ta daga harkokin zaben mu fiye da inda ake a dawo da shi a yau.

Abinda yafi komai a damukuradiya, wanda kuma yake sa a ci riba a damukuradiya shine a ba kowane dan kasar damar ya zabi shugaban da yake so, a zabe na gaskiya, da inganci ,ba magudi a ciki, Wanda dole a kaurace ma duk wata muzgunawa da cin mutunci.

Matsayin mu da muka more ma gyaran da akayi a hukumar zabe da tsare-tsare na rashin shiga hurdar wani yayin zaben, wanda ya zama abin misali da gwamnatin PDP da ta gabata tayi karkashin jagorancin Good luck Jonathan, ina tsammanin gwamtin APC zata gaggauta yima hukumomin tsaron gargadi.

In har gwamnatin APC ba zata iya habbaka  harkokin zabe ba, to ina tunanin da su barshi kan turbar da PDP ta yi.

In zaku iya tunawa hukumar zabe ta saka ranar Asabar 10, ga watan Satumba ta zama ranar da za'ayi zaben gwamna a jahar Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel