Karshen tsageru ya zo da murmushin kada -Buratai

Karshen tsageru ya zo da murmushin kada -Buratai

By-Babban hafsan sojin Najeriya ya ce karshen tsageranci ya zo

-Sojoji na da karfin da za su murkushe tsageru

-Buratai ya kaddamar wasu jiragen yaki a Kalaba

Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Buratai ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa, rundunar Sojin kasar na da karfin da za ta murkushe tsagerun yankin Niger Delta.

Karshen tsageru ya zo da murmushin kada -Buratai
Babban hafsan sojin Nigeria Buratai

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Babban hafsan sojin ya bayar da wannan tabbaci ne a a ranar Laraba 7 ga watan Satumba, a yayin ya ke kaddamar da yaki da tsageru a yankin, da aka yi wa lakabi da ‘Murmushin Kada’ a harabar makarantar koyar da dabarun yaki a ruwa da kuma tsandauri a garin Kalaba.

Buratai ya ce, aikin Sojoji ne samar da kuma wanzar da zaman lafiya, sannan ya kuma sha alawashin kawo karshen barnar da tsagerun ke yi a hanyoyin ruwa na kananan hukumomin Bakassi da Akpabuyo da ke jihar Kross Ribas.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun soma luguden wuta a kan tsageru

Janar Buratai ya kuma ce, “Mun kaddamar da murmushin kada ne a yankin Niger Delta saboda mu nuna cewa, ruwa ba sa an Kwando ba ne, mu kuma zakulo tare da damke duk wasu masu aikata laifi a yankin tare da ganin an hukunta su.”

Babban hafsan ya kuma kaddamar da wasu jiragen yaki guda 5 da kuma wurin gyaransu, a yayin bikin kaddamarwar,

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun fattaki tsageru daga bututun mai a Arepo

Ayyukan ta da kayar baya ya karu a yankin tun lokacin da Shugaba Muhammadu Bahari ya hau mulki, a inda a tsagerun suka rika farfasa butun Mai da na iskar Gas a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel