Dalilin da zai sa gwamnati kafa dokar ta baci kan wutar lantarki

Dalilin da zai sa gwamnati kafa dokar ta baci kan wutar lantarki

- Fred Majemite jigo ne na jam'iyyar People’s Democratic Party a jihar Delta.yayi kwamishinan kasa da kuma mai bada shawara kan harkokin siyasa ga tsohon gwamnan jihar Delta Emmanuel Uduaghan

- A wannan hira da yayi da Austin Oyibode na Legit.ng, yayi magana kan ci gaban jihar da kuma matsalolin da gwamnati mai ci ya kamata ta duba

Kayi aikin gwamnati na wasu shekaru, kayi kwamishina da mai bada shwara. A naka ra'ayin, wane cigaba aka samu jihar Delta tunda aka kikirota daga tsofuwar jihar Bendel?

Dalilin da zai sa gwamnati kafa dokar ta baci kan wutar lantarki

Ba zamu ce an sami biyan bukata ba, amma mun sami gagarumin cigaba. Yau muna zaune a jiha daya a matsayinmu na 'yan Delta. Bangaren ayyukan raya kasa, mun yi fiye da kima a nawa ma'aunin. Wajen gina jama'a akwai bukatar kara kokari , haka wajen kiwon lafiya ba laifi in ka dauki yawan asibitocin da muke dasu. Muna kuma da asibitin koyarwa.

Bangaren ilmi zan ce muna tsaka-tsaki, domin a cikin shekaru 25 kacal muna da makarantun fasaha guda hudu da jami'a daya mai harabobi ukku kuma dukkansu suna aiki kuma an amince da zamansu. Amma akwai bukatar maida hankali kan harkar noma inda ita kadai ce bamuyi abin azo a gani ba, abinda zai iya habaka tattalin arzikinmu, ya kuma samarma matasa ayyukan yi.

Na san gwamnati na iya kokarinta amma akwai bukatar wayar ma jama'a da kai domin yanzu an wuce loakcin neman aikin ofis, ya kamata mu koma gona. Akwai manyan gonaki na kasuwanci, kuma ya kamata gwamnati ta bude fili  yadda 'yan kasuwa zasu iya shigowa. A wajen gina gidaje bamu sami ci gaba ba, ya kamata gwamnati ta karfafa guyawun masu gina gidaje su saka jari wajen gidaje, akwai kuma bukatar amsar haraji domin bama biyan haraji

Mutane da yawa zasu ce kana fadin haka domin kana tare da gwamnati. Hanyoyi sun lalace, kuma ayyukan gina kasa sun tabarbarce?

Nace fiye da kima. Yanayin da muke ciki shi ke sa gyaran hanyoyin yaki yiwuwa. Kuma ba jihar Delta kadai ke da wannan matsalar ba, gwamnati bata da isassun kudi, saboda haka mamadin kashe duka kudin kan gyaran hanyoyi, sai ta kasasu yadda ko ina zai samu

Shekaru 25 bayan kafuwar jihar Delta, Assaba, babban birnin jihar bai kama da helkwatar jihar Delta ba. Magudanun ruwa sun lalace?

Har yanzu bamu ci nasara ba kan magudanun ruwa. Asaba nada tsarin raya ta, ya kamata ayi safiyo nagari domin fidda hanyoyin ruwa. Magudan da muke dasu basa iya daukar yawan ruwan da akeyi. Ya kamata muyi koyi da irin magudanun Onitsha.

KU KARANTA:Majalisar dinkin duniya tace kan yan Najeriya a rarrabe yake

Bangaren tsaro, ya ka kalli abin a jihar Delta?

Matsalolin tsaro abin damuwa ga dukkanmu, domin akwai yunwa a kasar. Maganinsa shine a jawo matasa. Amma yaya zaka iya jawo su yayin da baka da abin hannunka? Ya kamata mu taimaki gwamnati mu jawo mutane su saka jari cikin harkar noma inda za'a iya samarma jama'a aki ke nan domin kudin albashi kadai ya ishi gwamnati balle ta dauki ma'aikata. Abinda gwamnati zata iya yi shine ta taimaki jama'a su koma noma

Banbancin siyasar dake akwai da maganganun kiyayya da wasu keyi, kana ganin akwai hadin kan 'yan Delta masu manufa daya?

A matsayinmu na mutane, in da kammu ba hade yake ba, da yanzu mun dargaje. Zabe na karshe ya nuna mun fara yarda da juna domin gwamna bai ci zabe ba dalilin kuri'un Delta ta arewa ba, amma daga duk fadin jihar. Muna kallon kammu tamkar 'yanuwa. Abubuwan dake hada kammu sun fi masu rabamu

Me nene shawararka game da wutar lantarki?

Ya kamata gwamnati ta kafa dokar tabaci a wannan bangaren. Anyi haka a baya amma ban san inda aka kwana ba. Babbar matsala daya itace iskar gas, in an sami matsala a nan to za'a sami matsala da wuta. Da muka ziyarci Boeing a Amurka, kashi 60 na wutarsu daga madataun ruwa ne. Ya kamata mu fara tunanin mafita yayin da muke da isashen ruwa a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel